1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari´ar tsofan shugaban ƙasdar Irak Saddam Hussain

August 22, 2006
https://p.dw.com/p/Buly

Kotu a ƙasar Iraki ta koma sharia´a tsofan shugaban kasa Saddam Hussain, a game da tuhumar da aka yi masa ta hallala Ƙurdawa dubu 180, a shekara ta 1988.

Jiya ne, kotu ta fara wannan sabuwar shari´a, bayan wadda a ka yi wa Saddam da farko, a game da kissan gillan da ya wakana, kan mutane garin Dudajil.

Kotu ta ɗage zaman farko, bayan Saddam ya ƙi cewa ƙala a game da tuhumar da a ke yi masa.

A yau, ɗaya daga wanda su ka shigar da ƙara, ya bayyana gaban kotu, inda ya bada shaidu, masu tabbatar da cewa, Saddam Hussain ke da alhakin kai wannan hari.

Saidai tsofan shugaban ƙasar, da sauran mutane 6, da ake tuhumar su tare, basu ce komai ba, a game da wannan bayanai.

A ɓangaren tashe tashen hankullan da ya ke wakana a kasar, a yau sojojin Britania sun kai hari a birnin Amara dake tazara kilomita 400, a kudancin Bagadaza, inda su ka yi awan gaba, da wasu mutane 6, da ake ke zargi da aikata ta´adanci.

Sannan a birnin Bagadaza, duk da mattakan tsaron da aka ƙarfafa, ta hanyar jibge dakaru dubu 30, na Amurika da na rundunar tsaro ta kasa, har yanzu yan takife, na ci gaba da kai hare hare a wurare daban-daban.