1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shariar Saddam Hussein

Hauwa Abubakar AjejeJuly 10, 2006

Lauyoyi masu kare tsohon shugaban Iraki Saddam Hussein sun kauracewa sauraron karar tasa a yau yayinda a yau ne suke mika bayanansu na karshe a shariar ta saddam.

https://p.dw.com/p/BtzJ
Hoto: AP

Yawancin lauyoyin na saddam basu baiyana agaban kotun ba a yau,suna masu zanga zanga game da kashe daya daga cikin lauyoyin a watan daya gabata.

Batun kisan Khamis obeidi ya mamaye kotun a yau,yayinda lauya Ali Dayih Ali daya daga cikin lauyoyin yace babu hannunsa cikin kashe kashen 1982.

Cikin wata sanrwa da suka mika saoi kadan bayan bude shariar a yau,lauyoyin sun mika wasu bukatu 6 da suke nema a biya masu kafin su koma kotu,wadanda suka hada da tsaron lafiyar lauyoyin da iyalansu.

Hakazalika sun koka da tsoma baki na Firaminista Nouri al Maliki yayi game da shariar,musamman game da kalaman da yayi a farkon wannan wata,cewa yana fata zaa kashe Saddam ba tare da bata lokaci ba.

Cikin wani sabon matakin tsaro,baa nuna fuskan lauyan ba hakazalika an gurbata muryasa tan aura ba kamar shariar baya ba,inda ake nuna lauyoyin baro baro.

Lauya Najib al Nuemi daga Qatar ya baiyanawa kanfanin dillancin labaru na AP cewa,ba zasu baiyana a kotu ba har sai an biya masu bukatunsu,inda baya ga tsoron lafiyarsu da iyalansu,lauyoyin suna bukatar a sake dage shariar domin basu damar shirya jawabansu na karshe,yana mai cewa kashe al Obeidi da kuma batun rashin tsaro sun kawar da hankulan lauyoyin daga shiryawa yadda ya kamata.

Bayan bude shariar dai a yau babban alkali Raouf Abdul rahman,ya fara ne da mika taaziyarsa game da kashe lauyan,wanda shine na uku da aka kashe tun farkon shrair saddam da mukarrabansa a watan Oktoba.

Alkalin yace kotu tana Allha wadai da kowane irin hari akan lauyoyi ko maaikatan kotun.

Tunda farko dai masu daukaka kara sun bukaci a yanke hukuncin kisa akan saddam da dan uwansa Barzan al Tikriti da kashe yan shia 148 da ake zarginsu da aikatawa a kauyen Dujail a 1982.

Bayan jawaban karshe dai ana sa ran wani komitin lauyoyi 5 zai yanke hukunci,inda jamian koutu suka ce mai yiwune a yanke hukuncin nan da watan satumba.

Hakazalika kuma saddam da mukarraban nasa suna fuskantar wata shariar a ranar 21 ga watan agusta,game da zargin kisan kiyashi na dubban Qurdawa da sojojin saddam sukayi a 1988 a kauyukansu.

A wannan shariar dai mutum 7 ake sa ran zaa gurfanar cikinsu kuwa har da dan uwan Saddam din Barzan al-Majeed wanda caka fi sani da suna chemical Ali.

A yau din ma dai Saddam bai baiyana agaban kotun ba,haka manyan lauyoyinsa.

Komitin kare Saddam ta yanke cewa rashin lauyoyin Saddam a kotun,lauyoyin gwamnati zasu kare shi wanda kotu zata nada.

Komitin dai ya hada da,lauyoyi daga Amurka,Faransa,Lebanon da Jordan da kuma wasu larabawa,wadanda suka bukaci a dage sauraron karar har sai an kamala bincike game da musabbanin kashe lauya Obeidi.