Shari'ar Julia Timochenko
January 18, 2013Lauyan da ke kare madugar 'yan adawar Yukren Julia Timochenko, ya zargi hukumomin ƙasar da yin burus da matsanancin halin rashin lafiyar da ta ke ciki.
Yau ne ta kamata kotu ta yanke hukunci, game da zargin da a ke wa Timochenko na yin sama da faɗi da dukiyar ƙasa a lokacin da ta riƙe muƙamin Firaminista, amma a ka ɗage wannan shari'a har wata rana da a baiyana ba.
A zaman farko, kotu ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru Bakwai a gidan yari, sakamakon tuhumar da aka ma ta, na yin amfani da mulki fiye da ƙima, tsakanin shekara 2007 zuwa 2010.
Tun watan Mayu na shekara bara, a ka riƙe ta asibiti,sanadiyar ciwon baya.
Timochenko ta zargi gwamnatin Yukren da yin amfani da kotunan kasar domin ci mata zarafi.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman