1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan jaridun Jamus a kan Nahiyar Afirka

Usman ShehuNovember 29, 2013

Rikicin ƙabilanci da addini da na 'yan bindiga sun hana al'amura gudana a Jamhuriyar Afirka ta Tsakaiya, tun bayan tawayen da ya kifar da gwamnatin Faranscois Bozize

https://p.dw.com/p/1AQqa
Central African gendarmes patrol in Bangui on November 22, 2013. The sprawling country of five million people with a history of coups and rebellions has been beset by strife since the Seleka rebel coalition ousted president Francois Bozize in March and put the country's first Muslim leader, President Michel Djotodia, in power in the mostly-Christian country. In Bangui, killings have been blamed on ex-rebels of the Seleka coalition led by Djotodia before he dissolved it. To curb the unrest, Djotodia on November 22 said he was re-instating a curfew in Bangui from 10:00 pm to 6:00 am and on November 23, security forces could be seen on the major intersections of the capital. AFP PHOTO / PACOME PABANDJI (Photo credit should read PACOME PABANDJI/AFP/Getty Images)
Hoto: Pacome Pabandji/AFP/Getty Images

A cikin sharhuna na wannan mako, za mu farane da halin da ake ciki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda kusan dukkan jaridu suka mayar da hankali kan wannan ƙasa dake cikin yamutsi.

Sharhin jaridar Farnkfurter Algermeine Zeitung cewa ta yi. Ana fuskantar barazanar kisan kiyashi a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Sannan ta cigaba da cewa ƙasar Faransa zata tura sojoji 1000 zuwa babban birnin kasar Bangui, biyo bayan barazanar aukuwar kisan kiyashi. Ta ruwaito ministan tsaron ƙasar Faransa Eyves Le Drian na cewa, lamarin da ake ciki ya babbanta da ƙasar Mali, saboda a yanzu babu hukuma a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

epa03957914 Polling station staff assist voters during the municipal elections, in Maputo, Mozambique, 20 November 2013. Municipal elections in Mozambique took place amid tensions with the opposition Renamo party declaring that it was boycotting the vote. Earlier this year, Renamo was blamed for a series of attacks on convoys and railway lines. EPA/ANTONIO SILVA pixel
Hoto: picture-alliance/dpa

Tuni dai ƙasar Faransa ta aike da dakaru 450 zuwa Bangui, bayan ƙudurin da kwamitin sulhu na MDD ya gabatar bisa tura sojojin kiyaye zaman lafiya, babu bata lokaci kasar Faransa ta ayyana tura dakarun nata. Tun bayan kifar da gwamnatin Faranscois Bozize ne aka shiga ruɗani inda yan tawayen suka ƙwace mulki, suka kuma cigabada rike makamai.

Wanzuwar demokradiya a ƙasar Mozabik na tangal tangal, wanda shine sharhin da jaridar neues Deutschland ta yi. ta bada hujja kamar haka:

Babbar jam'iyar adawa ta RENAMO ta ƙauracewa zaɓukan ƙanan hukumomi da na kamsiloli da aka gudanar a faɗin ƙasar. Jam'iyya guda da ta samu tagomashi kan wannan zaben ita ce jam'iyar MDM, dake da kaso 42 cikin ɗari na ƙurin'un da aka kaɗa, yayinda jam'iyar Frelimo mai mulkin ƙasar tun samun yancin kai a shekara ta 1975, ta samu kashi 58 cikin ɗari na yawan ƙuri'un da aka kada yayin babban zabe a Moputo babban birnin ƙasar.

epa03474001 Refugees flee the fighting between the rebel M23 forces and forces loyal to the government hear Goma, Eastern Congo DRC, 16 November 2012. A weeks-long ceasefire in the eastern Democratic Republic of Congo appeared to be breaking down 16 November amid reports of troop movements and ongoing fighting between government forces and rebels. Late on 15 November, the M23 rebel group said it had come under attack from government troops and retaliated. Congolese government officials, who say the rebels attacked first, indicated dozens have died in the latest outbreak of violence. Thousands of refugees have fled the massive central African country to neighbouring Rwanda over the past few days, adding to the hundreds of thousands already displaced. Kigali is accused by the UN and Kinshasa of backing the M23 movement, which is largely comprised of ethnic Tutsis, like the Rwandan government. EPA/Alain Wandimoyi
Yan gudun hijiran KongoHoto: picture-alliance/dpa

Ita kuwa jaridar Bild Zeitung, ta rubuta labarinta ne kan yawan yan gudun hijra dake warwartse cikin ƙasar Yuganda. Jaridar ta bada misali da ƙauyen Bubukwanga, wanda ya cike ya batse da yan gudun hijira. A wannan ƙauyen in mutun ya je, babbu abinda zai gani sai bukkokin wucin gadi da tantuna, kana sai yara da ke wasa tumɓur, ko riguna ba su da shi. Dubban yan gudun hijira da ke wannan ƙauyen sun fito ne daga ƙasar jamhuriyar Demokraɗiyar Kwango, inda yaƙi ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, yayin da wasu bila'adadin suka tsere daga ƙasar zuwa maƙwabta.

Sai jaridar Die Tagestzeitung, wanda ta mai da hankali kan halin da ake ciki a gabashin Kwango. Jaridar ta yi tsokaci kan yadda yaƙin basa a ƙasar ya kawo lalata dazuka, da kuma kawar da namun dawa daga bainar kasa. Ta ce misali a ƙasar Kwango kusan kowa yasan hotunan dabbobi irinsu dangin jakin dawa, amma ƙalilanne suka taɓa ganinsu, domin jaridar ta ce manyan dazuka da ake da su kusan duk sun kasance fagen daga. Inda ta ƙara da cewa ga duk wanda ya tashi ya girma a waɗannan dazuka walau dai mutun ya kasance mai haƙar zinari da ake yi ta bayan fage, ko kuma ya kasance cikin ƙungiyoyin yan tawaye. A wani mataki na nuna mahimanci ga kare halittun dazuka da sauran dabbobin dawa, MDD ta sanyawa wata radio da ta kafa a kasar Kwango suna (Okapi) wato fitacciyar dabba mai kama da jakin dawa, da ke rayuwa a kungurmin dajin Kasar.