Sharhuna game da taron BRICS | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 29.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Sharhuna game da taron BRICS

A wannan mako jaridun Jamus sun fi mayar da hankali ga taron BRICS da juyin mulki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Da take tsokaci game da taron BRICS jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi, shugabanin kasashen Brazil,Rasha,China Indiya da Afrika ta Kudu sun shirya taro a birnin Durban na Afrika ta Kudu domin tattana halin da kungiyar BRICS ke ciki.Duniya ta zuba ido ta ga yadda za ta kaya game da kudurin shugabanin na kirkiro wata babbar Banki mai kama da Bankin Duniya ko kuma Asusun Bada Lamuni na Duniya, to amma daga karshe wannan yinkuri ya zama faduwar toto ruwa, domin taron ya watse ba tare da cimma nasarar wannan mataki ba.

Haka itama jaridar Neues Deutschland wadda ta ce kungiyar kasashen BRICS wada ta kunshi kashi 40 cikin dari na al'umar duniya,ta dauri aniyar kishi da Bankin Duniya da Asusun Bada Lamuni na Duniya ta hanyar kirkiro wata babbar Banki wadda za ta maida hankali wajen taimakawa kasashe masu tasowa, to amma a halin yanzu dai murna ta koma ciki duk da cewar ba a yanke kaunar ba zuwa gaba su girka wannan Banki.

A dangane da juyin mulkin da ya wakana a Jamhuriya Afirka ta Tsakiya,Süddeutsche Zeitung tambaya ta yi da cewa wai shin yaushe Jamhuriya Afirka ta Tsakiya za ta samu kwanciyar hankali ta fannin siyasa?jaridar ta ce tun lokacin da wannan kasa ta samu 'yancin kanta daga turawan Faransa ta ke fama da juyin mulki.Shugaba Francois Bozize wanda shima ya hau karagar mulki ta hanyar juyin mulkin ya bar mulkin ta wannan hanya a wani mataki mai cike da mamaki.Babban kalubalen da ke gaban saban shugaban kasa Michel Djotodia shi ne na farko maido doka da oda cikin kasa.

Itama jaridar Frankfurter Allgeimeine Zeitung, ta wallafa labari game da juyin mulkin inda ta ce masu kwasar ganima sun yi kaca-kaca da birnin Bangui.Jaridar ta ce akwai lauje cikin nadi game da wannan juyin mulki, ta la'akari da yadda cikin kiftawa da bismillah 'yan tawayen Seleka su ka yi nasara kifar da shugaba François Bozize duk kuwa da kasancewar sojojin Faransa da na kungiyar kasashen yankin Tsakiyar Afrika a cikin babban birnin.

Haka zalika jaridar Der Tagesspiegel cewa tayi ga alamu dai tsugunne ba ta kare ba a Jamhuriya Afirka ta Tsakiya domin a martanin da ta maida, Kungiyar Tarayya Afrika ta yi kira ga kasashen Afirka su maida Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya saniyar ware, sannan su dora takunkumi ga sabin jagororin kasar, idan dai har wannan mataki na gaskiya ne to kasar za ta fuskanci wani halin kunci,kuma matsalar za ta kare wa ne kan talaka wanda bai ci kasuwa ba runfuna ke fada masa.

Chief of the SELEKA rebel alliance Michel Djotodia sits on January 17, 2013 in Bangui during a ceremony. Opposition figure Nicolas Tiangaye was officially appointed today Prime Minister of the Central African Republic's new national unity government, President Francois Bozize said after a ceremony in the capital Bangui. The announcement was in line with a peace deal struck between the ruling party, the Seleka rebels and the democratic opposition in the Gabonese capital of Libreville last week.

Michel Djotodia

A wani bangaren jaridar die Tageszeitung tsokaci ta yi game da hukuncin da wata kotu ta yanke wa Henri Okah a kasar Afirka ta Kudu.

Bayan bincike, kotun ta samu Okah da hannu a cikin hare-haren bamai da wasu mutane suka kai a birnin Abuja a yayin da ake bukukawan samun 'yancin kan Najeriya ranar Daya ga watan Oktoba na shekara 2010.Jaridar ta ce tana gudun wannan hukunci ya bar baya da kura a Najeriya.

Za mu kammalla wannan shiri da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda ta yi sharhi game da hukuncin da Kotin Kolin Kenya ta yanke game da karar da Raila Odinga ya shigar domin kalubalantar zaben shugaban kasa da aka shirya a farkon wannan wata na Maris, inda ta ce al'umar Kenya ta ba marada kunya.Kotin Koli ta ya watsi da sakamakon wasu runfunan zabe kuma ta umurci a sake zabe a cikinsu, to saidai a cewar jaridar abin da kamar wuya saban zaben ya cenza jimlar sakamakon farko da hukumar zabe ta baiyana.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal