Sharhin jaridun Jamus kan nahiyar Afirka | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 26.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Sharhin jaridun Jamus kan nahiyar Afirka

A cikin sharhunansu na wannan makon kan nahiyar Afirka galibin jaridun Jamus sun maida hanakali kan bikin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta duniya, da batun dambarwar siyasa a Sudan haka da yawaitar hare-haren ta'addanci a Burkina Faso.

Saurari sauti 03:17

Bari mu fara da sharhin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta mai taken "Lokaci ya kure". Jaridar ta ce yayin da ake bikin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta duniya wato Malaria, abin na dada kamari. Jaridar ta ce kasar Mozambik ta fara cimma nasara. A shekara ta 2017, kasar ta Mozambik da ke yankin Kudu da Saharar Afirka ta kasance guda daga cikin kasashe ukun da cutar ta fi kamari a Afirka. Sai dai a 'yan kwanakin baya-bayan nan an samu ci- gaba mai ma'ana, inda a wasu yankunan kasar a iya cewa ba a ma asamu rahoton bullar cutar ba, kamar yadda  Christoph Benn na Asusun tattara taimako na kasa da kasa da aka kafa a shekara ta 2002 domin yakar cututtuakn HIV/ AIDs ko kuma SIDA da Tarin Fuka da kuma cutar ta Malaria a kasar. Sai dai sakamakon wata guguwa mai dauke da mamakon ruwan sama da ta haddasa ambaliyar ruwa, mutane da dama sun kauraacewa kauyukansu. A yayin da suka koma ana iya cewa akwai yiwuwar tuni tarin sauro da ke haddasa cutar ta Malria sun mamaye kauyukan.