1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka a jaridun Jamus na wannan makon

Mohammad Nasiru Awal LMJ
September 20, 2019

Halin da kananan yara ke ciki sakamakon tashe-tashen hankula a Afirka da Kuduna daga cikin abubuwan da suka dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3PxGk
Symbolbild Mexiko Geflüchtete aus afrikanischen Ländern
Mutane da dama sun shiga halin tasku sakamakon rikici a Afirka ta KuduHoto: Getty Images/Q. Blanco

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta leka kasar Afirka ta Kudu ta rubuta sharhinta ne tana mai cewa tashe-tashen hankula na ta'azzara a Afirka ta Kudu, lamarin da ke shafar kananan yara, sai dai hukumomi ba sa wani abin kirki don kawo karshen rigingimun. Jaridar ta ce a daidai lokacin da kyamar baki 'yan Afirka ta janyo asarar rayuka a Afirka ta Kudu, wata matsalar da kasar har yanzu ta kasa shawo kanta ita ce rigingimu tsakanin al'ummar kasar, inda kisan kai da kai hari da nufin kisa suka zama ruwan dare a unguwannin marasa galihu. Jaridar ta ce a baya-bayan nan a karshen wani mako guda lokacin da aka halaka mutane kimanin 70 a wata unguwar talakawa da ke birnin Cape Town, gwamnati ta girke sojoji. To sai dai jaridar ta kira matakin da wata alama da ta fito da rashin wani katabus daga bangaren hukuma don magance tashe-tashen hankulan tun daga tushe. Domin girke dakarun tsaron bai yi wani tasiri ba.

Sudan Khartum | Ex-Präsident Umar al-Baschir vor Gericht
Tsohon shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir ya gurfana gaban kuliyaHoto: Getty Images/AFP/E. Hamid

Dan kama karya a cikin keji wannan shi ne taken labarin da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta wallafa a tsokacin da ta yi na shari'ar da ake wa tsohon shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir a birnin Khartoum. Jaridar ta ce da kamata ya yi shari'ar da ake wa al-Bashir ta nuna alamar sauyi, amma sojoji sun yi mata babakere. Maimakon a dora masa alhakin aikata laifukan yakin da aka tabka a yankin Darfur da hannu a matakan ba sani ba sabo da aka dauka kan masu zanga-zangar da suka yi sanadin faduwar gwamnatinsa, yanzu hukumomin shari'a sun yi watsi da wadannan zarge-zarge sun mayar da hankali kan kyautar kudi daga kasar Saudiyya, da yawansu ya kai dalar Amirka fiye da miliyan tara da aka gano a gidansa cikin watan Afrilun da ya gabata bayan hambarar da shi. Jaridar ta ce rauni da ke tattare da hukumomin kasar ka iya silar barkewar sabon bore.

Ruanda-Rebellen von Sylvestre Mudacumura befehligt
Sylvestre Mudacumura jagoran 'yan tawayen FDLR ya kwanta damaHoto: AFP/L. Healing

A karshe sai jaridar Die Tageszeitung wadda a labarin da ta buga ta fara da cewa jagoran kungiyar 'yan tawayen FDLR ya rasu. Ta ce wani hoton da aka dauka na gawar Sylvestre Mudacumura da sanyin safiyar ranar Laraba a gabashin Kwango na zama shaida ta karshe da ta tabbatar da mutuwar daya daga cikin wadanda suka aikata laifukan yaki mafi muni a Afirka. Shi dai ya kasance hafsan soja, kuma shi ne jagoran kungiyar 'yan tawayen Ruwanda ta FDLR da ta kwashe shekaru gommai tana aikata ta'asa a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Jaridar ta ce wani hari na hadin gwiwar sojojin Kwango da na Ruwanda ne ya halaka jagoran 'yan tawayen a dajin Nyanzale da ke lardin arewacin Kivu. Tun bayan fara aikin sabon shugaban Kwango Felix Tshisekedi kasashen Ruwanda da Kwangon ke hada kai a yaki da kungiyoyin 'yan takife masu daukar makamai. Ita dai kungiyar FDLR bayan kisan kare dangi da ta yi wa 'yan kabilar Tutsi a Ruwanda, ta tsere zuwa makwabciyar kasa Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, inda ta sake hada kanta tana kuma kaddamar da hare-hare ba a kan Ruwanda kadai ba, kungiyar tana ma da hannu a kashe-kashen gilla a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.