1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sharhin Jaridun Jamus a kan Afirka

Usman Shehu Usman
October 11, 2024

Barazanar ta'addanci da sauyin yanayi na addabar al'ummar Mozambik

https://p.dw.com/p/4lhLc
Wasu daga cikin Jaridun Jamus
Wasu daga cikin Jaridun JamusHoto: Jan Woitas/dpa/picture alliance

Jaridar die tageszeitung ta yi sharhi ne kan siyasar kasar Mozambik inda aka gudanar da zaben shugaban kasa. Jaridar  ta ce ci gaba da barazanar ta'addanci da sauyin yanayi na addabar al'ummar Mozambik, amma ya kamata jam'iyyar Frelimo mai mulki ta sake lashe zabe a bana. Tun gabanin zaben ne dai aka baza karin jami'an tsaro, inda rahotannin suka ce akwai wuraren binciken da sojoji fiye da kowane lokaci kuma karuwar matsaloli tsaro ake so a kawar da wannan manufar ta baza sojoji, da kuma kawar da tashin hankali da ka iya faruwa bayan zaben. Jaridar ta ce duk wadannan matakai an gudanar da yakin neman zaben cikin lumana. amma Mozambik kasa ce mai saurin fada wa cikin rikici kasancewar ta yi shekaru baya cikin mummunan yakin basasa, ga kuma yanzu da masu ikirarin jihadi suka afka wa wani bangaren kasar.

Yan takarar shugaban kasa na 2024 a Jamhuriyar Dimukuradiyar Kongo
Hoto: ALFREDO ZUNIGA/AFP/Getty Images/Nádia Issufo/DW/Bernardo Jequete/DW/Cristiane Vieira Teixeira/DW

Sai kuma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wace ta ce kawo yanzu dai gwamnatin hadaka a kasar Afirka ta Kudu na da kwarin gwiwa bisa kwanaki 100 da tayi a kan mulki wato dai  "Gwamnatin Hadin Kan Kasa" ta na da kyau, a cikin kasar da ba a raba dukiya bisa tsarin da ya kamata, in ji jaridar. A ranar 29 ga watan Mayun 2024 ne shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da jam'iyyarsa ta ANC suka sha kaye. Jam'iyya mai mulki ta fadi daga kashi 57.7 a zaben da ya gabata zuwa kashi 40.2 cikin dari na kuri'un da aka kada. A karon farko tun bayan kafa mulkin dimukuradiyya a 1994, wanda kuma sakamakon zama dole jam'iyyar ANC mai fafutukar 'yanci a da ta raba madafun iko da sauran jam'iyyu.

Yawan hadarijn Jirgin ruwa a Jamhuriyar Dimukuradiyar Kongo
Yawan hadarijn Jirgin ruwa a Jamhuriyar Dimukuradiyar KongoHoto: Alain Uaykani/GOMA/Xinhua/picture alliance

Jaridar die Tageszeitung kuwa cewa ta yi, babbu ranar rabuwa da kisan mutane a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo. Jaridar ta ci gaba da cewa mako guda bayan da wani kwale-kwale ya nutse kan hanyarsa a kusa da gabashin Lardin Goma, har wannan ranar a ci gaba da arangama tsakanin wadanda suka tsira da kuma jami'an tsaro. Alkaluman hukuma suka ce kimanin miutane 34 suka mutu a nutsewar jirgin kuma kimanin mutane 500 sun bace. A bisa manufa dai, ya kamata a yi jimami a rana guda da aka ware a hukumance, amma sai aka samu ya rikide izuwa ranar yin bore. Matasa da manya sun yi ta kona tayoyi suna tare hanya. Masu boren daga bisani sun mamaye harabar dakin ajiye gawaki na birnin suna bukatar sai hukumomi sun bai wa ko wane iyali gawar mamatansu su binne a kauyukansu.