1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ayar tambaya kan makomar Birtaniya bayan zabe

December 13, 2019

Sau da yawa ana furuta kalamai irinsu abin al'ajabi, abin tarihi. Sai dai sakamakon zaben Birtaniya, zai sake fasalin siyasar kasar a shekaru masu zuwa a cewar Robert Mudge cikin wannan sharhi.

https://p.dw.com/p/3UmNz
Großbritannien Parlamentswahl Boris Johnson
Hoto: Reuterts/T. Melville

Kusan kowa ya san haka za ta faru, ko ba haka ba? A takaice dai lokaci na karshe da jam'iyyar Conservative ta samu irin wannan gagarumar nasar shi ne a 1987 karkashin Margeret Thatcher, wanda cikin murna ta nuna adawa da kungiyar EU, tana mai cewa a mayar wa Birtaniya da kudinta.

A wannan karon kalamai ne da ke cewa "A kammala Brexit." Sai dai za a dauki lokaci mai tsawo kafin hakan ta faru.

Deutsche Welle Robert Mudge
Hoto: DW

Shin alama ce ta wani lokaci na karerayi da alkawuran da ba a cikawa? Masu iya magana kan ce idan ana ta kai ba a ta kaya. Ilimi, miyagun laifuka, rashin gidaje ga jama'a da fannin kiwon lafiya da ya tabarbare kusan ba su dauki hankali masu zabe ba. Boris Johnson ya yi amfani da yaudara irin ta Donald Trump, babu kuma wanda ya nuna damuwa. Zai ci gaba da tabka karya cewa Birtaniya za ta fice daga EU cikin sauki za a kuma cimma yarjejeniyar kasuwanci kafin watan Disamban 2020. Sai dai ka da a manta EU da Kanada sun dauki tsawon shekaru 10 kafin sun amince da yarjejeniyar kasuwanci tsakaninsu.

Meye kuskuren jam'iyyar Labour? Ita kuwa jam'iyyar Labour mene ne kuskurenta? Ansar mai sauki ce wato Jeremy Corbyn. Shin jam'iyyar ta taba yin wani shugaba da ya raba kanta. Yayi tsammanin zai iya jan zarensa kamar a zaben 2017 lokacin da ya hana Conservative karkashin Theresa May samun rinjaye?

UK Wahlen 2019 | Jeremy Corbyn bei Auszählung
Jeremy Corbyn jagoran jam'iyyar LabourHoto: Getty Images/L. Neal

Yanzu Corbyn ba shi da zabi face ya sauka. ko da yake ya ce ba zai jagoranci jam'iyaar zuwa zabe na gaba ba, amma da kamata a ce yayi hakan tun gabanin wannan zaben. Jam'iyyarsa na dora lafin kayen da ta sha kan batun Brexit. Sai dai rashin kwarjinin shugabanta ya jawo mata wannan mummunan faduwa. Jam'iyyar ta kasa gabatar da wasu manufofi kwarara da za su samo hanyoyin magance matsalar tattalin arziki da kasar ke fuskanta karkashin Conservative ba. Jam'iyyar ta Labour na cikin matsaloli tana kuma kan hanyar rugujewa.

Makomar Birtaniya a fagen siyasar duniya Ana iya cewa zaben tamkar wata gasa ce ta rashin farin jini, kuma Boris Johnson ya yi nasara. Shin akwai wanda ya yarda cewa Johnson zai cika alkwuran da ya dauka? Gaskiya babu, sai dai masu zabe sun fi damuwa da alkawuran Jeremy Corbyn ya yi.

Großbritannien Boris Johnson nach der Wahl 2019
Boris Johnson Firaministan BirtaniyaHoto: Reuters/D. Martinez

Abin da ya fi damuwa na zama illar da sakamakon zai yi a kasar da tuni kanta ya rarrabu. Da alama yankin Scotland ya amsa kiran da Jam'iyyar Scottish National Party ta yi cewa suna son sake karbar ikon yankinsu. Ko shakku babu za su matsa kaimi na gani an sake gudanar da kuri'ar raba gardama karo na biyu kan 'yancin yankin. Tabbas gwamnati za ta yi adawa da wannan mataki. Amma tuni har an fara daukar wannan mataki domin Babbar Ministar Scotland Nicola Sturgeon ta ce Firaminista Johnson ba shi da ikon cire kasarta aga kungiyar EU. Ko masu kishin kasa na Ireland da suka sami yawan kuri'u a zaben su ma za su nemi a gudanr da zaben ficeewar yankin daga Birtaniya?
Sakamakon zaben na ranar Alhamis ya nuna makomar Birtaniya a fagen siyasar duniya, ya kuma bude sabon babi na sauyin siyasar Birtaniya da zai dauki hankali a kasar cikin shekaru da yawa masu zuwa.