1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Hari kan Abiy Ahmed

June 23, 2018

An kai wani mummunan hari kan sabon Firaministan kasar Habahsa, dama a 'yan kwanakin bayannan ne aka gargadi sabon fiiraministan kasar ta Habasha cewa da ya bi sannu-sannu a shirinsa na kawo sauyi a kasar.

https://p.dw.com/p/309kL
Äthiopien Kundgebung Premierminister Abiy Ahmed in Addis Ababa | Explosion
Hoto: Oromo Media Network

A sharhin da shugaban sashen Amharic na DW Ludger Schadomsky ya rubuta ya fara da cewa,  Babu dai bukatar tambaya bisa irin sauye-sauyen da ya kawo. Ya soke dokar ta-baci, dubban fursunonin siyasa an sake su, an fara kawo sauye-sauyen a bangare rundunar soja da jami'an leken asiri, bangaren tattalin arziki an fara sassauta wa jama'a, sai kuma gashi an shirya da makobciyarsu Iriteriya. Wadannan duk cikin karamin lokaci, abin da ba'a zata ba a kasar da ke mulkin demokradiya amma cikin tsattsauran ra'ayi. 

Abin da ake zaton dai ya faru kamar yadda wani mai lura da siyasar kasar ya fada a ranar Juma'ar da ta gabata, cewar yunkurin kawar da mai kokarin kawo sauyin na kara bayyana, kuma ga harin neman hallaka shi ya tabbata. Gangamin miliyoyin 'yan kasar da aka yi a wannan Asabar, wata babbar dama ce ta miliyoyin kasar da su bayyana goyon bayansu ga dan kasar mai shekaru 42 da haifuwa, wanda ya shirya kawo sauyi, abinda ke sa tsoro ga zukatan gungun masu wawurar dukiyar kasar da shugabannin siyasa wadanda suka kankane al'amuran kasar ta Habasha. Masu halartan gangamin sun sa rigunan da aka rubuta kalmomin nuna goyon baya ga kawar da wadannan da suka hana ruwa gudu a kasar. wato kama daga shugabannin hukumomin leken asiri, shugabannin bankuna da gwamnonin jihohi. 

Gaba tsakanin juna

Hari kan Firiminista wani "yunkurin masu adawa da zaman lafiya ne" wadanda ke kokarin wargaza hadin kan kasar, wannan shi ne abin da firaministan da ya tsallaka rijiya da baya ya bayyana, bayan an jefa gurneti kan gangamin jama'a. Hakan dai wani fama ciwo ne da tsohon sojan Abiy ya yi. Kasar da yanzu za'a ce tana cikin wani gausti, inda a shekarun baya ba'a batun hada kan 'yan siyasan kasar, a kasar da ke da al'umma kimanin miliyan 100.

Tun lokacin da a ka fara kada guguwar sauyi da shugabannin sabuwar gwamnati suka kawo, ake ganin gungun mutanen da suka kankane mulki sama da shekaru 25, yanzu lokacin kakkabe hannayensu ya zo karshe. Don haka ake ta yin rade-radin me ka iya faruwa, tsakanin masu yukurin samar da demokradiyya da kowa zai amfana, da kuma wadanda za su rasa madafun iko in hakan ta samu, ana ganin wannan matakin ne da ba shi da tabbas. 

Äthiopien Demonstration Untersützung für Premierminister Abiy Ahmed in Addis Ababa
Hoto: picture-alliance/Anadolu Agency/M. Wondimu Hailu

A yanzu dole a jira aga abin da kwanaki da ke tafe za su kawo. Idan dai har yadda ake rade-radin cewa jami'an tsaro ne suka kitsa harin, to hakan zai gamu da fushin akasarin 'yan Habasha masu yunkurin kawo sauyi. Idan kuma wata kungiya ce wace jami'an tsaron ke mara wa baya, to hakan zai kara ingiza rikicin kabilancin kasar. 

Ga shi dai "Mai ceto" Abiy Ahmed kamar yadda wasu ke kiransa, abin da ya faru a wannan Asabar ya kara karfafa masa gwiwa, na ci gaba da kawo sauyi, domin dama mai yin gyara na tattare da adawa. Abiy wanda shi ne firaministan farko daga kabila mafi girma ta Oromo, a watannin da suka gabata ya tara makiya da yawa. Wannan ya isa ya dan sassuata kokarinsa na kawo sauye-sauye. An cusa kabilanci a sauye-sauyensa, kamar yadda ya fada bayan harin. "Ku da ke son raba kanmu yanzu na gano ku. Anniyarku ta wargaje"