1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Aikin jarida na bukatar kariya

May 3, 2018

Peter Limbourg shugaban tashar Deutsche Welle, ya yi sharhi kan ranar 'yancin ‘yan jarida ta duniya, yayin da tashar ta Deutsche Welle ke cika shekaru 65 na wannan aiki.

https://p.dw.com/p/2x2cl
Berlin Tag der Pressefreiheit
Hoto: Imago/IPON

Ranar uku ga watan Mayu na kowace shekara rana ce da aka kebe kan bikin 'yancin 'yan jarida. Wannan abu ne mai kyau, saboda a kalla sau guda an tuni da 'yancin dan Adam. Sai dai sau tari 'yancin 'yan jarida kan zama abu mai dadin fada. Sauran ranaku 364 na shekara babu mai nuna wata damuwa game da haka, kamar yadda shugaban gidan rediyon DW Peter Limbourg ya rubuta a cikin sharhinsa a wannan rana.

Ana iya ganin zahirin haka bisa yadda 'yan siyasa na kasashen Turai ke rige-rige aiki da kasar China. Kasar da aka dakile 'yancin 'yan jarida kuma aka toshe kafofin yada labarai kamar tashar DW da sauran na kasashen ketere ko kuma suna sahun baya. Manyan 'yan kasuwa sun fi mayar da hankali kan kasuwanci da China ya zama abin da aka bai wa fifiko maimakon kare hakkin dan Adam. Karkashin haka mahukuntan birnin Beijing suka mamaye komai. Saboda a China babu wanda zai tayar da jijiyar wuya idan aka samu rashin jituwa da masu zuba jari na kasashen ketare.

Wani abun mamaki 'yan siyasa na Jamus da kasashen Turai ke neman ganin an fahimci Shugaba Vladimir Putin na Rasha duk da dari-darin da yake da shi kan kungiyar tsaro ta NATO da Tarayyar Turai. Yayin da tsoron da 'yan jarida ke da shi a daya hannun a Rasha ya zama abin tayar da hankali da ake a boye, don tsoron cin zarafi gami da yiwuwar rasa rai. Sai dai sabon ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya dauki matsaya ta daban.

Toshe kafofin yada labarai na ketare

Israelische Bodenoffensive im Gazastreifen - Journalisten auf Aussichtspunkt an der Grenze
'Yan jarida kan yi aiki cikin dari-dariHoto: picture-alliance/ dpa

A kasar Iran kuwa mahukunta na toshe yunkurin kafofin yada labarai na DW da sauran kasashen ketare tare da musguna wa ma'aikatan. Zai yi wuya a yi maganar 'yan jarida 23 da dakarun juyin-juya hali suka gana wa azaba a gidan fursuna. Duk da haka 'yan siyasa na tunanin kulla hulda da gwamnatin, wadda take neman lalata Isra'ila da taimakon ta'addanci a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.

A kasar Saudiyya an yaba wa yerima mai jiran gadon sarauta saboda damar da mata suka samu na tuka mota,a lokaci guda Raif Badawi mai rubutu ta kafar sadarwa ta Internet yana fursuna saboda fadin albarkacin baki.Masu mulkin sai madi ka ture na Afirka suna nema tarewa da samun karin makudan kudaden taimakon raya kasa, yayin da suke hana matasa 'yan jarida shan iska musamman na kafofin masu zaman kansu.

A kasashen Bangaladash da Pakistan masu rubutu a kafofin zamani na Internet kan fuskanci barazanar rayuwa saboda masu kaifin kishin addinin Islama da ke kara samun  gidin zama a kasar. Gagarumin taimako daga kasashen ketare ya yi karanci duk da yunkurin jami'an diplomasiya.

Kawance da kasashe da ke hana 'yan jarida walwala

Mexiko tana cikin masu shirya bikin baje koli a birnin Hannover na Jamus a shekara ta 2018. Wannan kasa ce da ke sahun gaba inda 'yan jarida ke cikin hadari saboda gwamnati ta gaza shawo kan masu safarar miyagun kwayoyi. 'Yan jarida 11 aka kashe a shekarar da ta gabata, a Siriya kadai aka samu adadi da ya haura haka. Manyan kasashen sun fahimci nauyin da ya rataya a wuyansu kan haka. Abun takaici shi ne jerin bai tsaya haka ba, domin kasashen kungiyar NATO akwai Turkiya yayin da Poland da Hangari ke cikin mambobin Kungiyar kasashen Tarayyar Turai.

Ya dace a rika gwada gwamnatoci bisa mizanin abin da suka yi domin kare 'yancin 'yan jarida. A sassan duniya demokaradiyya na fuskantar barazana daga 'yan kama karya da 'yan kishin kasa. Kuma za a samu nasara ce idan aka nuna tirjiya. Wannan bikin ya zo lokacin da tashar DW ta cika shekaru 65 da fara yada labarai zuwa sassan duniya, kuma za ta ci gaba da tabbatar da kare 'yancin 'yan jarida.