1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Shaka: Sarkin al'ummar Zulu

Thuso Khumalo AT Bala/SB/MNA
September 10, 2020

Sunan Shaka Zulu na da nasaba da yaki. Dakarunsa kan tarwatsa duk wanda ya sha masa gaba. DW ta yi hira da masanin tarihi Maxwell Shamase wanda yake ganin an gurbata tarihin Shaka.

https://p.dw.com/p/3iCmX
African Roots | Shaka Zulu | Porträt

An fadi abubuwa da dama game da Shaka Zulu. Idan ana batun bambance gaskiya da kagaggen labari, Maxwell Zakhele Shamase mashahuri ne. Shi da Mthandeni Patrick Mbatha, masanin tarihi daga jami'ar Zululand a yanzu haka su na rubuta wani littafi a kan mutumin da ke zama gwarzon tarihi.

 

DW: Me ya sa za ku rubuta tarihi game da Shaka Zulu?

Maxwell Shamase: Ba a yi wani rubutu mai yawa a game da Sarki Shaka musamman daga mahanga ta Afrika ba. Wasu daga cikin abubuwa wadanda mutanen da ba 'yan Afirka ba suka rubuta, a gurbata gaskiyar lamura a cikinsu. Muna so mu bayar da labarin daga mahanga ta yan Afrika.

Yaya za ka baiyana Sarki Shaka?

Kafin a haifi Shaka, wata bokanya mai suna Sithayi, ta ba da labarin cewa za a haifi wani yaro wanda zai kawo sabon sauyi da kuma sabuwar kasa. Ya kasance soja dan baiwa a Afirka. Mutum ne wanda ya gina kasa ba mai son kisa da zubar da jini ba. Kuma ba mutum ne mara tausayi dan inda da kisa ba.

Yaushe ne kuma a ina aka haifi Shaka?

An haifi shi a watan Juli shekarar 1787 a cikin al'umar eLangeni inda mahaifiyarsa ta fito.

Ina Shaka Zulu ya samo sunansa?

Mahaifinsa mutum ne mai aiki da hankali (Senzangakhona). Mahaifiyarsa 'yar sarkin Nandi ce a gidan sarautar Mhlongo wanda ya rayu a wurin da ake kira eLangeni. Sunan Shaka ya samo asali ne daga wata cuta da ake kira ishaka. Wannan cuta na sanya jikin mata ya rika ciwo da kasala da kuma kumburi. A lokacin da mahaifiyarsa wace a wancan lokaci ba ta yi aure ba ta samu ciki, mutane sun yi tsammanin tana fama ne da cutar ishaka. Yadda Shaka ya sami wannan sunan kenan.

Shaka Zulu: Basaraken al'ummar Zulu

Saboda haka ya kasance Shaka dan Senzangakhona. A wancan lokaci sunan mahaifinka shi ne sunanka na biyu. Kuma sunan kakan Shaka shi ne Zulu. Lokacin da Zulu ya zama sarki, sai Shaka ya ce ya kamata mu sami al'adarmu mu kira kanmu mutanen Zulu. Shi ne na farko da ya kira jama'arsa mutane Zulu, shi ya sa aka san shi a matsayin wanda ya kafa kasar Zulu duk da cewa ya gaji sarautar da ta dade tsawon zamani.

Shin mahaifin Shaka, Senzangakhona, ya amince dansa ne?

Ya yi ta kokarin musantawa saboda yana tsaron mahaifinsa, Sarki Zulu. Ga yarima mai jiran gadon sarauta kamar Senzangakhona ya yi wa yarinya ciki kafin aure abin kunya ne wanda ka iya kaiwa ga hukunci mai tsanani ciki har da yiwuwar rasa damar yin sarauta. Daga baya iyayensa suka amince kuma Senzangakhona ya biya kudin sadaki wanda ya bai wa Nandi damar tarewa cikin iyalan Senzangakhona.

Daga bayan an fitar da Nandi da Shaka daga gidan Senzangakhona, Shin ya ya aka yi haka ta faru?

Nandi mace ce mai dagawa da saurin fushi da so a kullum ta rika bai wa mutane umarni. A saboda haka dangantakarsu ta kasance cike da rigingimu. Senzangakhona ba zai iya jurewa ba. Ya kore ta tare da Shaka. Sun yi ta watangaririya. Nandi ta hadu da Ngwati. Suka fara soyayya su ka cigaba da zama tare inda ta haifi kanwar Shaka.

Bayan da aka kashe Ngwati, Sarkin Mthethwa Dingiswayo ya karbi 'ya'yanta biyu. Yaya aka yi Shaka ya shiga cikin rundunar sojin Mthethewa?

Ya zama babban yaron Sarki Dingiswayo a lokacin da ya ke dan shekaru 16 da haihuwa. Wannan kuwa ya kasance ne saboda basirarsa da kuma karfin zuciya. Ba a jima ba aka dauke shi a matsayin mayaki aka sa shi cikin rundunar Izicwe.

Wane tasiri Shaka Zulu ya yi a rundunar sojin Mthethwa?

A matsayin kwamanda ya hana mayakan sanya takalmi fade ya kuma uamrcesu su rika tafiya babu takalmi. Haka kuma ya hana amfani da dogon mashi wanda mayaka za su habi abokin gama da shi. Maimakon haka, ya bullo da gajeren mashi ‘Iklwa'domin fada dab da dab da abokin gaba. Wannan ya tilasta wa mayakansa su matso kusa su sari abokin gaba sannan su juya su sari wani da makami daya. Ya kuma bullo da dabarar raba mayaka dama da hagu domin yi wa abokan gaba kofar rago. Tsarin ya yi kama da yanayin kahuna biyu na karkanda. Ya zama mutumin da ake matukar jin tsoronsa wanda kuma ya yi fice hatta a sauran kabiluda masarautu, a kan haka ne ma ya sami sunan 'Nodumehleli' wanda ke nufin "wanda daga zaune ya ke sa duniya ta girgiza". 

Mayakin Mthethwa shi ne wanda a karshe Shaka ya danka wa sarautar Senzangakhona. Shin babu wanda ya kalubalanci wannan mataki?

A lokacin da mahaifinsa Senzangakhona ya rasu, Sarki Dingiswayo ya taimaka masa dawowa wajen al'ummar mahaifinsa inda ya ba shi mayaka biyu su taimaka masa karbe ragamar mulki. Sai dai Senzangakhona ya fada wa babban wazirinsa cewa daya dan nasa Sigujana shi ne yarimansu mai jiran gado amma ba Shaka ba. Da isarsa sai ya kashe Sigujana kuma ya karbi karagar mulki a shekarar 1816 a matsayin Sarki. Bayan mutuwar Sarki Dingiswayo, Shaka shigar da mutanen   Mthethwa karkashin daularsa sannan ya kabilar da Dingiswayo ya ci da yaki cikin sojojin da ke karkashin jagorancin Shaka. Ya kuma cigaba ya ci sauran kabilu da yaki ya kuma mulkesu.

Shaka na da mummunan tunani kan aure, inda har ta kai wasu mutane na cewa mai yiwuwa dan luwadi ne shi. Menene dalilin haka?

Mummunan tunaninsa ga aure ya faru ne sakamakon yadda ya ga aka yi wa mahaifiyarsa. Sannan an ci zalinsa matuka sakamakon tasowa da ya yi ba cikin danginsa ba kuma ba tare da mahaifinsa ba. Babu shakka ya yi jima'i da mata to amma da zarar sun sami ciki sai ya mika su ga dan uwansa, Mpande wanda ake gani a matsayin rauni.

Gaskiyai ne cewa Shaka Zulu yana kashe matan da ya yi wa ciki, kamar yadda aka yi ta rade-radi?

Wannan ba gaskiya ba ne. Mun dai san cewa akwai wani lokaci da wasu 'yan kasuwa farar fata suka farfado da wata mata da ta suma saboda zazzabi mai zafi. Shaka da mutanensa sun yi tsammanin ta mutu. Sun ba ta magani su ka farfado da ita. Shaka ya zaku ya na so ya tabbatar ko da gaske ne yan kasuwar sun tayar da matacce. Ya bada umarnin a kashe wata mata sannan ya umarni yan kasuwar su nuna ikonsu su tayar da ita wanda ko shakka babu baus iya yin hakan ba. A wasu lokuta saboda son ganin kwakwaf, an shaida mana cewa ya fede cikin wata mace mai ciki domin ganin yadda jariri ya ke girma a cikin ciki.

Mun ji cewa Shaka ya kashe mutane kusan miliyan daya, wasu daga cikinsu haka kawai ko kuma wai saboda sun yi gajarta. Shin gaskiya ne?

Wannan tunani ne na kasashen yamma, kuma ba gaskiya ba ne. Ka tuna mutane miliyan 50 suka mutu a yakin duniya na biyu baya ga wasu miliyoyi da suka rasa rayukansu a yakin duniya na daya. A saboda haka wane ne ya fi rashin imani tsakanin Shaka da wadannan Turawa da suka haddasa yakin duniya na daya da na biyu? To amma ya kamata a dauki kisan da aka aikata a wannan hali a yanayi na lokaci. Abu ne da mutane su ka saba da shi a wancan lokaci. Zai bada dalilai da su ka sa aka aikata kisan. Alal misali, wadanda aka tabbatar da cewa mayu ne an kashe su. Sarakuna a wancan zamani sun dore ta hanyar kashe abokan hamaiyarsu.

Wata hanya aka kashe Shaka Zulu?

An kashe shi a cikin watan Satumba shekarar 1828. Akwai wani makirci da aka shirya bisa jagorancin goggonsa. Babban dalili shi ne bayan mutuwar mahaifiyarsa Nandi, Shaka ya samu tabin hankali inda ya kashe mutane da dama ba tare da yin tunani ba inda ya fake da jimamin mutuwar mahaifiyarsa. Wasu ya kashe su ne saboda sun ci zalinsa a lokacin da yake dan yaro, yayin da wasu kuma aka kashe su saboda ba su nuna alhini sosai game da rasuwar mahaifisarsa ba.

Shin matsala ce a kira Shaka ‘Baki ko kuma Napoleon din Afirka?

Gwarzon soja ne dan baiwa na Afirka ba bakin Napoleon ba. Me ya sa ba za a ce da Napoleon farin Shaka ba? Bai taba zuwa Turai ba kuma babu wani Bature da ya koyar da shi abubuwan da ya yi a fagen yaki. Sun fito ne daga baiwar da yake da ita.

Ko har yanzu Shaka Zulu ya na da tasiri a yau?

Shi ne jigon hadin kan Zulu. Jam'iyyar Inkatha Freedom Party wadda ta mamaye Kwazulu Natal ta danganta kanta da Sarki Shaka a matsayin tushenta. Sarakunan Zulu da al'ummarsu suna yin mubaya'a ga sarautar Sarki Shaka har zuwa yau.

Maxwell Zakhele Shamase, kwararren masanin tarihin Zulu yana da digirin digirgir a tarihi da siyasar wannan zamani da kuma tarihin al'ummar Zulu. A yanzu haka yana rubuta wani littafi a kan Sarki Shaka. H Shamase shi ma malami ne kuma shugaban tsangayar koyar da tarihi a jami'ar Zululand wanda har ila yau ake kira Unizulu.

Shawarwari da suka danganci kimiyya a wannan kasidar, an same su ne daga masana tarihi Farfesa Doulaye Konaté, da Dr Lily Mafela, da kuma Farfesa Christopher Ogbogbo. Tushen Afirka na samun tallafi ne daga gidauniyar Gerda Henkel.