Shafukan sada zumunta sun sake daukewa | Labarai | DW | 09.10.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shafukan sada zumunta sun sake daukewa

A karo na biyu a cikin mako daya Facebook ya sake katsewa bayan da masu amfani da shafukan WhatsApp da Messenger da Instagram suka kasa aike da sakonni na wasu lokuta a daren Juma'a.

Tuni kamfanin ya nemi afuwar miliyoyin kostomominsa da abin ya shafa kai tsaye tare da ba da tabbacin shawo kan matsalar bayan faruwar sa. "Muna mai neman afuwa ga duk wanda bai sami damar shiga shafukanmu ba a cikin awanni biyu da suka gabata, mun gyara batun, kuma komai ya kamata ya dawo dai-dai yanzu." Inji kakin kamfanin na Facebbok lokacin da ya ke magana da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP da misalin karfe 11:30 na daren Jumma'a agogon GMT.

Wannan dai na faruwa ne kwanaki kadan bayan Facebook ya fuskanci irin wannan matsalar katsewa mafi girma da ya sa ta yi asarar sama da dala biliyan bakwai tare da jefa kananan 'yan kasuwa cikin rudani.