Sha′anin tsaro a Mali bayan nasara akan ′yan tawaye | Labarai | DW | 31.01.2013
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sha'anin tsaro a Mali bayan nasara akan 'yan tawaye

EU ta nemi dakarun Afirka su hanzarta karbar alhakin tsaro a Mali daga hannun Faransa.

Ministocin kula da harkokin wajen kasashen kungiyar tarayyar Turai, wadanda suka gana a wannan Alhamis, sun bukaci dakarun kasashen Afirka su hanzarta karbar ragamar kula da harkokin tsaro a kasar Mali, ba tare da wani bata lokaci ba.

Ministan kula da harkokin wajen Beljiam, Didier Reynders, wanda kasarsa ta kudiri anniyar ci gaba da tallafawa Faransa a irin matakan sojin da take dauka a kasar Mali - har ya zuwa ranar daya ga watan Maris, ya ce Turai na fatan cewar, nan bada dadewa ba, samame a kasar ta Mali, zai kasance wani alhaki ne daya rataya a wuyan daukacin kasashen duniya, wanda kuma zai sami goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, yana mai cewar musamman ma aikin zai kunshi sojojin kasashen yankin ne.

Shi kuwa ministan kula da harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, cewa ya yi abu mafi a'ala a yanzu shi ne kyalewa dakarun Afirka su jagoranci harkokin tsaron, wanda ya ce zai zama sauki ne ga ita kanta Faransa.

Sai dai takwaran aikinsa na Austria Michael Spindelegger, ya yi gagadin cewar mika harkokin tsaron ga dakarun Mali, ba mai yiwuwa bane anan kusa.

Nan gaba a wannan Alhamis ne ministan wajen Faransa Laurent Fabius, zai yiwa takwarorin aikinsa na kasashen Turai 27 jawabi dangane da ci gaban da aka samu a kasar ta Mali.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu

 • Kwanan wata 31.01.2013
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17VMS
 • Kwanan wata 31.01.2013
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17VMS