1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Vucic: Zanga zanga tada zaune tsaye ne

Abdullahi Tanko Bala
July 9, 2020

Hukumomin kasar Serbia sun haramta taron jama'a da ya wuce mutum goma a Belgrade babban birnin kasar bayan shafe kwanaki biyu ana dauki ba dadi tsakanin 'yan sanda da dubban masu zanga zangar adawa da dokar kulle. 

https://p.dw.com/p/3f4X0
Serbien I Ausschreitungen in Belgrad
Hoto: Reuters/M. Djurica

Hukumomin kasar Serbia sun haramta taron jama'a da ya wuce mutum goma a babban birnin kasar Belgrade bayan shafe kwanaki biyu ana dauki ba dadi tsakanin 'Byan sanda da dubban masu zanga zangar adawa da dokar kulle. 

Gwamnatin ta ce an kafa dokar ce domin dakile yaduwar annobar cutar corona.

Shugabar kasar ta Serbia Aleksandar Vucic ya yi kakkausar akan masu zanga zangar wadanda ya baiyana a matsayin 'yan tada zaune tsaye.

Hukumomin na nazarin dawo da dokar takaita zirga zirga a karshen mako wadda ita ce ta haifar da tarzomar tun da farko.