Senegal ta ba wa hambararren shugaban Guinea-Bissau mafaka
November 28, 2025
Hukumomi a Senegal sun tabbatar da isar hambararren shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo, inda zai ci gaba da samun mafakar siyasa bayan kifar da gwamnatinsa.
Juyin mulki a kasar Guinea-Bissau
Ma'aikatar harkokin wajen Senegal ce ta tabbatar da isar Mista Embalo a kasar, inda ta ce ya sauka Dakar, a cikin aminci da koshin lafiya, bayan ta aike da wani jirgin ya dauko shi daga Bissau babban birnin kasar Guinea.
Sojoji sun hambarar da gwamnati a Guinea-Bissau
Duk da duniya na suka da caccakar juyin mulkin ciki har da Majalisar Dinkin Dunia da ta bukaci a dawo kan turbar dimukuradiyya cikin gaggawa, sabon madugun juyin mulkin kasar Janar Horta N'Tam, ya karbi ranstuwar kama aiki, inda ya bayyan cewa zai jagoranci gwamnatin rikon kwarya ta shekara guda.
Kura ta lafa a Guinea-Bissau bayan juyin mulki
Tuni jam'iyyar adawa sun ki amincewa da juyin mulkin, suna mai bayyana hakan a matsayin wata kullalliya don hana tabbatar da sakamakon zaben da ya ba su nasara, suna masu kira da a gaggaua mika musu mulki.