1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawa sun lashe zaben kananan hukumomi a Senegal

Abdourahamane Hassane
January 25, 2022

Kawancen jam'iyyun siyasar da ke yin mulki a Senegal sun sha mummunar kaye a zaben kananan hukumomi da aka yi a karshen makon jiya.

https://p.dw.com/p/463aW
Senegal Coronavirus l Präsident Macky Sall
Hoto: Ludovic Marin/Pool/REUTERS

A manyan birane kasar irinsu Dakar da Thiess hadin gwiwar jam'iyyun siyasar da ke yin mulkin sun rasa mazabu da dama masu mahimmanci a gaban jam'iyyun siyasar masu hamayya da gwamnatin wadanda suka hada da na Usman Sankon. Wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben shugaban kasar da ke tafe. Wannan zabe ana yi masa kallon zakaran gwajin dafi ga zaben na shugaban kasar da za a yi a shekara ta 2024 a Senegal din.