Seleka ta nemi Shugaba Samba Panza da ta yi murabus | Labarai | DW | 09.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Seleka ta nemi Shugaba Samba Panza da ta yi murabus

Bayan wa'adin da 'yan Anti-Balaka suka bayar, daga nasu bangare 'yan kungiyar Seleka, sun nemi Shugabar rikon kwarya Catherine Samba Panza da ta yi murabus.

Hakan dai ya zo ne a dai dai lokacin da wasu sabbin tashe-tashen hankula tsakanin kabilu suka yi sanadiyar mutuwar mutane bakwai a Bangui babban birnin kasar. Da yake magana da kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP, Younous Ngardia, mashawarci a kwamitin koli na kungiyar ta Seleka, ya ce sun yi matukar mamakin ganin yadda shugabar ta rikon kwarya ta aiko biyar daga cikin membobin gwamnati zuwa gare su kan cewa 'yan kungiyar Seleka su fice daga birnin Bambari da ke tsakiyar wannan kasa, inda ake yawan samun tashe-tashen hankula tsakanin kabilu. Dama dai a farkon wannan mako ne 'yan kungiyar Anti-Balaka suka bai wa shugabar rikon kwaryar kasar wa'adin kwanaki biyu na ta yi murabus.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo