Seleka ta ki amincewa da sabuwar Firaminista
August 11, 2014'Yan tawayen Seleka na arewacin jamhuriyar Afrika ta tsakiya sun yi fatali da yunkurin kafa gwamnatin hadaka, kasancewar ba a tuntubesuba kafin zabin sabuwar firaministar, abin da suke cewa zai sa su sake nazarin yarjejeniyar tsagaita wuta da suka kulla a watan da ya gabata.
Shugaba mai ci Catherine Samba Panza ta bayyana Mahamat Kamoun a matsayin wanda aka dora wa alhakin kafa gwamnati da zata samu karbuwar jama'ar kasar, ta kuma kai kasar ga gudanar da sabon zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa. Wannan dai na daga cikin irin matakan da gwamnatocin ke bi wajen kawo karshen kisan gilla da ake yi a wannan kasa da ya yi sanadin mutuwar dubban jama'a da sanya kimanin mutane miliyan daya kauracewa muhallansu.
Kamoun masanin tattalin arziki, ya kasance jagoran majalisar zartarwar kasar a lokacin gwamantin Micheal Djotodia, amma 'yan tawayen sun bayyana cewa ba mamba ba ne na kungiyar Seleka.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Pinado Abdu Waba.