SDFna babban taro duk da barazanar tsaro | Labarai | DW | 22.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

SDFna babban taro duk da barazanar tsaro

Jam'iyyar SDF da John Fru Ndi ke shugabanta a kamaru ta bai wa marada kunya na gudanar da babban taronta duk da barazanar kai mata hari da 'yan awaren yankin da ke magana da Ingilishi suka yi.

Wahl in Kamerun

Babbar jam'iyyar adawa ta Kamaru SDF ta yi nasarar fara babban taronta a birnin Bamenda da ke yammacin kasar duk da barazanar gurgantashi da 'yan aware suka yi sakamakon zarginta da zama 'yar amashin shatan gwamnati. Shaguna sun kasance a rufe a birnin bisa kiran masu rajin dara Kamaru gida biyu, lamarin da ya tilasta wa shugabannin SDF canja wurin taro zuwa babban zauren taro na Bamenda.

'Yan Ambazoniya sun yi barazanar kai hari idan jam'iyyar SDF ta kuskura gudanar da babban taron saboda tana bai wa gwamnatin da suka danganta da ta 'yan tawaye hadin kai. Ita dai Jam'iyyar da ke a matsayi na biyu a yawan 'yan majalisa a Kamaru za ta yi amfani da babban taron nata wajen gudanar da zaben fidda dan takarar da zai tsaya mata a zaben shugaban kasa mai zuwa. Sai dai a karon farko madugun 'yan adawan Kamaru Ni John Fru Ndi yana fuskantar hamayya mai tsanani daga mataimakinsa Joshuah Osih.