Sauye-sauye a tsarin samun bayyanai a Amirka | Labarai | DW | 10.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sauye-sauye a tsarin samun bayyanai a Amirka

Shugaba Barack Obama ya yi alƙawarin ƙaddamar da sabon tsarin na naɗar bayyanan sirri a wani abin da ya kira tabbatar da haske domin samun yardar jama'a.

Shugaban wanda ya bayyana haka a wajen wani taron manema labarai da ya yi, ya ce zai yi aiki da 'yan majalisun ƙasar domin kai wa ga yin sauye-sauye a wani ɓangaren dokar yaƙi da ta'addanci. Sannan ya ce zai ƙara matsa ƙaimi ga ƙudirin nan, na musamman wanda zai bai wa gwamnati samun damar bayanai ta hanyar sauraron wayoyin tarho na jama'a da ake kira da sunnan Patriot Act. Wanda ya ce ke zaman wata hanya ta yaƙi da ta'addanci amma kuma tare da kula da 'yancin yin walwala na jama'a kana kuma ya ƙara da cewar.

''Za mu iya, kuma ya kamata mu ƙara tabbatar da haske a cikin wannan al'amari na tatsar bayyanan sirrin wanda babu wani sauran yin rufa-rufa.''

Sauye-sauyen sun biyo bayan fallasa bayyanan sirri na satar sauraran wayoyin jama'a da hanyoyin sadarwa na yanar gizo da gwamnatin Amirkar ta riƙa yi. Wanda tsohon jami'in hukumar leƙen asirin ƙasar Edward Snowden ya tsegunta wa jaridun wasu ƙasashe.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal