1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zazzabin cizon sauro na cigaba da illa ga jama'a a Nijar

Abdourahamane Hassane
October 4, 2019

Shirin Lafiya Jari ya dubi yadda zazzabin cizon sauro ke illa ga lafiyar jama'a da matakan kariya da hukumomin kiyon lafiya ke dauka don kare al'umma. Sai a saurari shirin don jin karin bayani

https://p.dw.com/p/3QkSE
Mücke Malaria
Hoto: picture-alliance/dpa/P. Pleul

Yanzu haka a wasu sassa na Jamhuriyar ana cikin hali na tsanani na fama da cutar zazzabin cizon sauro wacce ta ke hadddasa babbar ila a kan sha'anin kiwon lafiya, ko da yake hukumomin kiwon lafiya sun bayyana daukar matakan rarraban gidan sauro ko sange kyauta ga jamaa da sauran magungun a domin yaki a cutar da ta yi sanadiyar muutuwar mata da yara.

Sau tari a cikin irin wannan lokaci na bayan damina lokacin girbe amfani gona sauro ya fi damun jama'a wanda kuma ya janyo babbar larura ta cutar malariya. A wani asibibin da ke zaman kansa na afuwa dake  a birnin Damagaram na Jamhuriar Nijar Likita dokoto Basahir Yayaha ya ce a kulum sun kan samu kusan mutum 50 wadanda ke zuwa karbar magani bisa kamuwa da zazzabin na cizon sauro.Domin yaki da wannan cutar hukumomi a jihar a Damagaram na yankin Zinder sun kaddamar da shirin rarraba gidan sauro sangi da magungna ga jamaa kyauta domin yin riga kafi ga kamuwa ga cutar ta azabin cizon sauro wacce ke kara ta'azzara.

Niger - Gesundheitsstation in Garin Goulbi
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Schulze

Sakamakon yadda cutar ta yi kamari a yanzu ya sa iyaye mata a tsakaninsu sun kafa tsarin fadakar da sauran al'umma mahimmncin zuwa ganin likita da kuma saka yara gidan sange don kare lafiyarsu daga cutar ta zazzabin cizon sauro. 

Likitoci da hukumomin kiyon lafiya sun bayyana cewa shiga gadan sange da tsarin wayar da kan jama'a zai taimaka sosai a cimma nasarar yaki da cutar to amma kuma sun ce dole sai jamaa sun kara dagewa.