Saudiya ta daure masu ra′ayin jihadi | Labarai | DW | 08.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saudiya ta daure masu ra'ayin jihadi

Mahukunta a Saudi Arebiya na kara tsaurara matakai na tsaro dan kauce wa masu akidar kaifin kishin addinin Islama ko 'yan jihadi.

Kronprinz Abdullah von Saudi Arabien

Wata kotu ta musamman a kasar Saudi Arebiya ta yanke hukuncin zama a gidan kaso na tsawon shekaru 6 ga wasu mutane da suka aikata laifuka da ke da alaka da tsaro, ciki kuwa harda zuwa kasashen waje dan halartar yaki da debo akidu na mayakan sakai, abinda kafar yada labaran kasar ta bayyana da "rashin biyayya ga shugaba".

A watan da ya gabata wannan daula ta yanke hukuncin zama a gidan kaso ga mutane da dama a wasu shari'u da aka yanke masu alaka da batun na tsaro saboda fargabar cewa rikicin da ke faruwa a Iraki da Syria na iya cusa akidar neman tashin hankali a zukatan matasa a kasar ta Saudiya.

A watan Fabrairu ne dai Sarki Abdallah ya bada umarnin daurin shekarun 3 zuwa 20 ga duk wanda ya tafi wata kasa dan halartar yaki, sannan za'a kuma daure duk wanda aka kama da laifin ya bada tallafi ga wata kungiya mai tsatstsauran kishin addini daga shekaru 5 zuwa 30.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal