Saudiya na luguden wuta a Yamen | Labarai | DW | 26.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saudiya na luguden wuta a Yamen

Wasu kasashen Larabawa da taimakon kasar Amirka sun kaddamar da harin jiragen sama a kasar Yamen, inda kasar Saudi-Arabiya ke jagorantar farmakin

A daren jiya ne dai aka fara luguden wuta kan mayakan Huthi na kasar ta Yamen. Inda akalla fararen hula 13 suka mutu, wasu da damam suka jikkata. Yan tawayen Huthi dai sun kwace Sana'a babban birnin kasar, tun a watan Satumba, kuma yanzu suna kara nausawa izuwa birnin Aden mai tashar jiragen ruwa da ke kudancin Yamen. A cewar kasar Saudiyya dai ta shiga yakin Yamen ne, domin ta kare halartaccen gwamnatin kasar da Abdo-Rabbo Mansur Hadi, ke jagoranta. Tuni dai kasashen Jordan, Masar, da Morocco suka sanar da shiga yakin da kasashen 10 suka kaddamar kan kungiyar Huthi a Yamen. Ita kuwa kasar Amirka ta tabbar da bada taimakon kayan yaki da bayanen sirri.