Sauƙaƙa wayar salula a ƙasashen EU
September 11, 2013Ƙungiyar Tarayyar Turai na tsara wani shiri da zai bai wa masu amfani da wayar salula a stakanin ƙasashen ƙungiyar 28, damar buga waya a ko wace ƙasa tamkar suna ƙasashensu na asali, wato babu ƙarin kuɗi, wanda ake ƙira Roaming a turance. Wani daftarin da majalisar dokokin ƙungiyar EU ta fitar, ya ce idan aka samar da shirin, to a duk ƙasashen EU 28 za ka buga waya tamkar a gidan ka. Wannan tsarin wata babbar han'ya ce ta sauƙaƙa buga wayar tafi da gidanka a ƙasashen na Tarayyar Turai, inda kusan kowa ya mallaki wayar salula. Ministan sadarwa a hukumar EU Neelie Kroes ta ce manufar shirin ita ce bai wa 'yan ƙasashen mambobin ƙungiyar damar cin moriyar buga waya, ba tare da ƙarin wani cajin kuɗi ba, ta yadda ba za a yi la'akari da ga ƙasar da mutun yake ba.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammed Nasir Awal