1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sassou-Nguesso na kan gaba a zaben Kwango

March 22, 2021

A yayin da ake ci gaba da kirga kuri'u a kasar Kwango Brazzaville, sakamakon farko na nuna cewa shugaban kasar Denis Sassou-Nguesso ne ke kan gaba a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Lahadin karshen mako. 

https://p.dw.com/p/3qyaf
Republik Kongo Wahlen Brazzaville
Hoto: Hereward Holland/REUTERS

Sakamakon tuni hukumar zaben kasar ta fara sanarwa na nuna cewa shugaba Sassou-Nguesso na kan gaba a gomman gundumomi, inda tuni ya samu nasarar kashi 85% a wasu gundumomi hudu. Shugaban mai ci a yanzu na neman karin waa'din shugabanci na hudu a kasar bayan shafe shekaru 36 a mulki.

Ranar Laraba ne hukumar zaben Kwango Brazavile za ta sanar da cikakken sakamakon zaben shugaban kasa. Amma 'yan adawa da kungiyoyin farar hula sun zargin bangaren gwamnati da aringizon kuri'u, tare da bayyana hukumar zaben kasar a matsayin 'yan korar gwamnati.