Sassauta dokar hana zirga-zirga a Wukari | Labarai | DW | 23.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sassauta dokar hana zirga-zirga a Wukari

Gwamnatin jihar Taraba ta ce daga wannan Alhamis al'ummar Wukari na iya fita daga karfe shida na safe izuwa sha biyu na rana. Wato suna da sa'o'i shida na yin zirga-zirga.

Kamar yadda Sakataren watsa labaran gwamna mai rikon gwamnatin jihar, Mr. Kefas Sule ya shaida wa wakilinmu Muntaqa Ahiwa, yanzu jama'ar Wukari na iya walwala daga karfe 6 na safe zuwa karfe 12 na rana.

Kefas Sule ya ce gwamnati ta yi zama ne da sarakunan gargajiyar yankin na Wukari kafin a kai ga wannan matsaya, ta kuma yi nadamar irin tsananin da dokar ta yi wa jama'a. Gwamnatin ta kuma ce ana iya kara sassauta ta, muddin aka sami kwanciyar hankali da ta gamsar.

Al'umar Wukarin dai sun koka kan tsananin wannan dokar da aka kafa ba fita dare da rana. Inda jama'a suka ce kama daga na karancin abinci da ruwan sha da ma na bullar wasu cututtuka.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasiru Awal