1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarrafa garin wake domin abinci

November 14, 2018

Wani matashi da ya kammala digirinsa ya rungumi sana'ar yin garin wake don saukaka wa al'umma samun cimaka cikin sauki.

https://p.dw.com/p/38EYS
Uganda - Super beans
Hoto: DW/F. Yiga

Wani matashi da ya kammala digirinsa ya rungumi sana'ar yin garin wake don saukaka wa al'umma wajen samun cimaka cikin sauki.

Koda yake matashin Hamza Shehu Aliyu yace ya jingine kwalin digirinsa ya rungumi wannan sana'ar sakamakon  sha'awar da yake da ita ta yin sana'a tun yana dan karami.

Tuni dai matashin yace ya samu alfanu sosai bayan shafe shekara daya yana gudanar da sana'ar?

Yanzu hakama dai matasa da dama ne ke aiki karkashin kanfanin wannan matashi Hamza Aliyu                                                 

Ta fuskar kalubale kuwa  matashin yace yaci karo da  karancin kudi amma hakan bai hana hakarsa cimma ruwa ba, inda ma matashin ya ja hankalin 'yan uwansa matasa masu dogon buri ba tare da aiwatar da wani  abu ba su yi hobbasa.na