Sarkin Maroko ya yi amai ya lashe | Labarai | DW | 05.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sarkin Maroko ya yi amai ya lashe

Zanga-zangar 'yan Maroko ta tilasta wa Sarki Mohamed na Shida soke afuwar da ya yi wa Daniel Galvan Vina dan kasar Spain.

Spanish prime minister Mariano Rajoy (L) speaks with Moroccan King Mohamed VI during a meeting in Rabat, Morocco, 18 January 2012. It is Rajoy's first official visit as Spanish prime minister. EPA/CHEMA MOYA Schlagworte Diplomatie, Diplomatie)

Mariano Rajoy Mohamed VI

Bisa matsin lambar al'umar kasa, Sarki Mohammed na VI na Marroko ya soke afuwar da ya yi wa Daniel Galvan Vina, wani dan kasar Spain, wanda kotu ta yanke wa hukuncin shekaru 30 a kurkuku, bayan ya amsa lefin lalata da kananan yara akalla 11, 'yan shekaru hudu zuwa 15.

Idan dai ba a manta ba, a makon da ya wuce ne, Sarki Mohamed na VI, ya sa hannu kan dokar afuwa ga wasu 'yan asulin kasar Spain, dake zaman kurkuku a Maroko, da zumar kara inganta ma'amala tsakanin kasashen biyu.

To sai dai afuwar ta bar baya da kura, ta la'akari da yadda zanga-zangogi suka barke a sassa daban-daban na kasar, domin nuna fushi ga belin Daniel Galvan Vina, mai shekaru 64 a duniya.

A wani abu mai kama da ihu bayan hari, tuni Galvan Vina ya riga ya fita daga kasar ta Maroko.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal