Sarkin Kano Sanusi ya shiga gidan sarauta | Labarai | DW | 13.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sarkin Kano Sanusi ya shiga gidan sarauta

Mai Martaba Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya shiga fadarsa da ke tsakiyar birni bayan rikicin da aka yi fama da shi a jihar sakamakon nada shi.

Bayan tsawon kwanaki ana sa toka sa katsi, yanzu haka dai sabon sarkin Kano mai martaba Malam Sanusi Lamido Sanusi ya shiga fadarsa da ke tsakiyar birnin Kanon na Dabo. Da yammacin wannan Jumma'ar ne dai sabon sarkin wanda ya sa fararen kayan kawa kuma akan farin Doki, ya yi tattaki daga fadar gwamnatin jihar i zuwa ainihin fadar sarkin Kano.

Tuni dai aka sara wa sarkin sabuwar kofar da ya shiga ta cikinta, daga nan ne kuma ake sa ran zai zauna a soron Malam Dabo, inda zai ci gaba da addu'a na tsawon kwanaki, kafin ya kammala da wasu al'adu na masarautar.

Kafin shiga gidan dai sabon sarkin Kano ya jagoranci sallar Jumma'a a masallacin Jumma'a da ke gidan gwamnati, inda a cikin hudubarsa ya yi kira ga al'umma da su zauna lafiya da juna tare da bayyana muhimmancin hakuri. Wannan dai ya kawo karshen dambarwa da zaman dar-dar da rashin shigar Sarki Sanusi Lamido Sanusi gidan sarauta ya kawo a Kano.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Suleiman Babayo