1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Beljium: Takaicin azabtarwa mulkin mallaka

Abdullahi Tanko Bala
June 30, 2020

A karon farko a tarihin kasar Belgium sarkin da ke kan mulki ya baiyana takaici game da azabtarwar da tsofaffin 'yan mulkin mallakar kasar suka aikata a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo.

https://p.dw.com/p/3eatU
Belgien König Philippe Rede Anschläge Brüssel
Hoto: Reuters/N.Maeterlinck

A cikin wata wasika da ya aike wa shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Felix Tshisekedi, Sarki Philippe na Belgium ya nuna matukar takaici da cin zarafi da azabtarwa da Belgium ta aikata wa jama'a a Kwango, sai dai bai nemi afuwa ba a hukumance.

An wallafa wasikar a wannan rana da kasar ta Kwango ke bikin cika shekaru 60 da samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka.

Sarki Philippe ya baiyana fatan kyakkyawar dangantaka a tsakanin kasashen biyu ba tare da nuna wariya ba. Ya kuma ce domin karfafa dangantakar da ke tsakaninsu, wajibi ne su gayawa juna gaskiya game da abubuwan da suka faru a baya.