Sarkakiya game da zaben Madagaskar | Siyasa | DW | 31.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sarkakiya game da zaben Madagaskar

Yayin da ake cigaba da kidayar kur'un da aka kada a zaben kasar Madagaskar, alamu na nuna cewar za a iya tafi zagaye na biyu na zaben kafin a kai ga samun shugaban kasa.

Daga cikin 'yan takara 33 da ke zawarcin kujerar shugaban kasar ta Madagaskar dai ana kyautata zaton Jean Louis Robinson da yanzu haka ke da kashi 28 cikin 100 na rabin kuri'un da aka kidaya, da kuma Hery Rajaonarimampianina wanda ke da kashi 15 cikin 100 na kuri'un ne za su fafata a zagaye na biyu na zaben wanda ke tafe cikin watan Disamba mai zuwa.

Wahlen Madagaskar Richard Jean Louis Robinson

Richard Jean Louis Robinson

Jean Louis Robinson dai tsohon ministan wasannin da kiwon lafiya na kasar ne kuma na hannun daman tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana wanda aka hana yin takara a zaben, yayin da Hery Rajaonarimampianina ke zaman tsohon ministan kudi wanda shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar Andry Rajolina ke marawa baya.

Dangantaka tsakanin wadannan 'yan takara ce ma ta sanya al'ummar kasar wanda kashi 90 cikin dari ke cikin kangi talauci ke ganin cewar ba za ta sake zani ba dangane da irin shugabancin da za a iya girkawa.

Wannan ne ma ya sanya Sahondra Rabenarivo lauya kuma 'yar rajin kare hakkin bil adama a kasar ganin cewar zaben tamkar takara ce tsakanin Ravalomanana da Rajolina.

Wani abu kuma da ke daukar hankalin al'ummar kasar da masana harkokin siyasa gami da wanda suka sanya idanu a zaben na Madagaskar shi ne irin yadda uban gidan siyasa na wanda ya lashe zaben zai amfani da wannan dama wajen cimma wasu buruka nasa.

Marcus Schneider na gidauniyar Fredrich Ebert da ke nan Jamus na daga cikin wanda suka suka sanya idanu a wannan zabe. Ya ce "dantakarar da Mr. Ravalomanana ke goyawa baya wato Jean Louis Robinson ya bayyana cewa aikinsa na farko bayan ya lashe zabe shi ne nada mai dakin shi Ravalomanana a matsayin firaminista, na biyu kuwa shi ne maido Ravalomanana gida daga gudun hijirar da ya ke yi.

Wannan ya sanya gwiwar al'ummar kasar yin sanyi domin kuwa Mr. Ravalomanana ka iya yin amfani da goyon bayan da zai iya samu in Mr. Robinson ya lashe zabe wajen yin ramuwar gayya na abubuwan da aka yi masa bayan da aka hambarar da shi daga gadon mulki.

Wahlen Madagaskar Hery Rajaonarimampianina

Hery Rajaonarimampianina

Shi kuwa Mr. Rajaonarimampianina a nasa bangaren ya ce zai yi aiki ne da shugaba Rajoalina, lamarin da ya sanya al'ummar kasar ke cewar in haka ta tabbata to shakka babu mafarkinsu na samun sauyi na tsarin shugabanci ba zai taba zamowa gaskiya ba.

To sai da Marcus Schneider na gidauniyar Fredrich Ebert na ganin cewar ko ma waye ya lashe wannan zabe da ma irin zubin da zai yi wajen shugabantar kasar nasara ce ta al'ummar kasar domin kuwa za a kafa gwamnati ce wadda jama'a suka zaba ba wadda ta dare gadon mulki da karfi tuwa, batun ya sanya Marcus din cewar kimar kasar za ta dawo a idanun duniya watakila har ma hakan a kai ga cire mata takunkumin da aka kakaba mata.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin