1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Sarauniya Abla Pokou: Uwar al'ummar Baoule na Ivory Coast

Julien Adayé ATB/MNA
December 24, 2020

Abla Pokou sarauniya ce ta Akan wadda ta jagoranci jama'arta daga kasar Ghana ta yanzu zuwa Ivory Coast a 1770, tarihi ya nuna ta sadaukar da danta ga iskoki domin mutanenta su ketara kogi.

https://p.dw.com/p/3nCMT
African Roots | Abla Pokou

Mene ne matsayin Abla Pokou a cikin al'ummar Ashanti?

An haifi Abla Pokou a matsayin Gimbiya a farkon karni na 18. 'Ya ce ga dan uwan sarki Osei Tutu — wanda da shi aka kafa daular Ashanti da ta zama kasar Ghana a wannan zamani. A lokacin da ya rasu rikicin shugabanci ya barke aka kashe Dakon dan uwan Abla Pokou wanda yana daga cikin masu gadon sarauta. A bisa tsoron rayuwarta da danginta Abla Pokou ta gudu.

 

Wane ne ya yi wa Abla Pokou rakiya a lokacin da ta tsere?

Abla Pokou ta gudu tare da dukkan mutanen da suke biyayya ga Dakon wanda kuma ya ki amincewa Opokou Ware ya gaji sarauta. Ta hada gagarumar runduna ta kuma jagorancin tawagar zuwa inda a yanzu kasar Ivory Coast ta ke.

 

Ta yaya Abla Pokou ta je Ivory Coast?

Tarihi ya ruwaito cewa lokacin da suka tsere, sarauniya Abla Pokou da magoya bayanta sun kasa cigaba yayin da suka isa kogin Comoe. Comoe dai nan ne kan iyaka tsakanin kasar Ghana ta yanzu da kuma Ivory Coast.

Kogin ya cika makil saboda ruwan sama da ake yi akai akai, a saboda haka ba za su iya tsallakawa ba. Sarauniya Abla Pokou ta shawarci Bokan da ya yi musu rakiya, sai yace aljanun kogi sun bukaci a sadaukar da jariri. Sai Abla Pokou ta jefa danta cikin kogin kuma ya bace a kogin da ke kara yin toroko.

Duk da haka a cewar wani kaulin na tarihi, wani abin mamaki ya faru, bishiyoyin da ke gabar kogin sun rankwafa suka yi gada. Wani kaulin kuma yace manyan Dorinar ruwa ne suka fito suka yi jerin gwano suka yi musu gada yadda Abla Pokou da yan rakiyarta za su iya wucewa.

Bayan da suka tsallaka, Abla Pokou ta rusa kuka tana kuwwa ta "Bâ wouli" ma'ana "Jaririn ya mutu". Wannan kalmar mai yiwuwa ita ce ta samar da sunan Baoule ("ba wouli") al'ummar, al'ummar da a yanzu ta ke zaune a Ivory Coast.

 

Shin tabbas Abla Pokou ta sadaukar da danta a cikin kogi?

"Sarauniya Abla Pokou mai yiwuwa ba ta sadaukar da jariri ba", a cewar farfesa Kouamé René Allou kamar yadda ya shaidawa DW. "Akwai wasu lokuta a cikin shekara da kogin Comoe kan janye yadda za ka iya taka duwatsun da ke karkashin kogin ka ketara." Mai yiwuwa wannan shi ne abin da Baoule ta yi a cewar wasu majiyoyi.

Sarauniya Abla Pokou: Uwar al'ummar Baoule a Ivory Coast

Ina ne hakikanin inda Abla Pokou ta zauna a lokacin da ta isa Ivory Coast?

Sarauniya Abla Pokou ta zauna a yankin Namounou da ke Bwake kusa da kauyen Akawa. Namounou na nufin "kula da uwa", ya kamata mutane su kula da Abla Pokou a wannan wuri. 

Abin takaici, an kaura cewa kauyen Namounou bayan da sarauniyar ta rasu. An binne ta a cikin kogin N' draba. Akawa Boni, wanda ya gaje ta ya tashi ya koma Sakassou da zama.

 

Yaya ake tunawa da ita a yau?

Har yanzu ana tuna sarauniya Abla Pokou ta hanyar adabin baka da kuma adabin zube a Ghana da Ivory Coast sai dai kuma yana da wuya iya samun hotunan Abla Pokou.

Babu wani gini ko gidan tarihi da aka sanya wa sunan ta baya ga wani mutun-mutumin karfe da ke dandalin République da ke Abidjan. Sai dai kuma a fagen kayan kawa wasu masu tsara kayan kwalliyar sun samar da salo masu yawa dauke da sunan shahararriyar sarauniyar Abla Pokou.

Shawarwari ta fannin kimiyya ga wannan mukala an same su ne daga masana tarihi Farfesa Doulaye Konaté, Lily Mafela, Ph.D., and Professor Christopher Ogbogbo. Tushen Afirka na samun tallafi daga gidauniyar Gerda Henkel Foundation.