Sandy ta hadasa mumunar ɓarna a Amirka | Labarai | DW | 31.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sandy ta hadasa mumunar ɓarna a Amirka

Al'amuran sufirin jiragen sama da na ƙasa sun tsaya cik, sakamakon mahaukaciyar guguwar wacce ba a taɓa ganin irin ta ba cikin shekaru da dama da suka wucce

Miliyoyiin jama'a ne a yankin kudu maso gabashi na Amirka suka kwana cikin duhu, sakamakon tsimkewar wutar lantarki da layukan sadarwa na telho,biyo bayan mahaukaciyar guguwar nan ta Sandy da ta yi mumunar a jihohin New Jersey da New York.Magajin garin birnin New York Michael Bloomberg ya ce suna ƙoƙarin samar da wutar lantarki a cikin kwanaki biyu biyu ko ma fiye da haka

An shirya shugaba Barack Obama wanda ya katse kampe ɗin sa,zai ziyarci jihar New Jersey wacce ya yi ikirari a matsayin jihar da bala'i ya aukawa, da ita da New York .Mutane kusan guda 40 guguwar ta kashe daga cikin su 18 a New York.Yayin da da sama da miliyion takwas na iyale basu da wutar lantarki a yanki arewa maso gabashin na ƙasar.Ƙwarraru sun ce za a yi ƙiesta asarar kamar ta biliyan dubu 20 da wannan guguwa ta hadasa, wacce a yanzu ta doshi ƙasar Canada.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas