Sana′ar Cukwi na habaka a Kwango | Himma dai Matasa | DW | 21.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Sana'ar Cukwi na habaka a Kwango

Duk da irin kalubalen rashin kwanciyar hankalin da ake fiskanta a kasar Kwango wani malami, ya habaka sana'ar sarrafa cukwi har 'yan uwansa na mamaki.

Mazauna tsaunukan gabashin Kwango na samun kudin dogaro da kai ta hanyar sarrafa cukwi daga shanun da suke kiwatawa, sun kuma rungumi wannan tsohuwar sana'ar gargajiyar da zai kare yankin daga yakin da suke fama dashi. Nan inda Niyetegeka Canisius ke aikin sarrafa madarar Cukwi ke nan daga nonon da yake tatsa daga shanun da yake kiwo. Kuma Canisius yanzu ya yi sama da shekaru ashirin yana wannan sana'ar.

“Wanna bangaren shi ke da mahimmanci a aiki baki daya, saboda nan ne na ke kada madarar sannan cukwin yayi kwari.”

Canisius dai dan asalin tsaunukan da ke arewacin Kivu ne, wanda ke da tazarar kilomita 50 daga yankin Goma. Ko da yake Canisius ya yanke kafa da zuwa yankin, tun bayan da 'yan bindiga da suka addabi yankin a shekarun baya, to amma yanzu dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya na kokarin tabbatarda tsaro a yankin.


Aiki tare da masu wanzar da zaman lafiya

Tare da taimakon wadannan dakarun wanzar da zaman lafiya da ke yaki da masu hako ma'adinan zinari da ke da alhakin illolin da ake samu a yankin, a yanzu dai Canisius na habaka aikinsa na sarrafa cukwi tare da 'yan uwansa ba tare da fargaba ba, wanda hakan ke ba su damar sarrafa madarar cukwin da dama, a yini guda. Canisius dai na alfahari da wannan aiki na sarrafa cukui, ganin yadda sana'ar ke rufamasa asiri da iyalansa.

Africa on the move

Gonar Niyitegeka Canisius a yankin arewacin Kwango

"Burina kenan tun ina yaro in ga na sarrafa cukwi. Madarar tana da dandanon gaske sannan ga lafiya, shi ya sa kwalliya ke biya min kudin sabulu a sana'ar.”

Tallafin wani dan Beljiyam


Ko da yake dai wani dan Beljiyam ne tushen sarrafa madarar cukwi a Congo, sannan akayi amanna da dandanonsa. To amma Canisius kadan ne daga cikin wadanda suka maida hankali wajen yadda ake sarrafa madarar ha rma al'ummar yankin ke yabawa.

“Ban dai san yadda ake sarrafashiba, to amma ianjin dadinsa matukar gaske.”


Canisius na gudanarda kasuwancin cukwi a yankin Goma shekaru da dama, inda yake saida kowani kilo kan kudi Euro 2 zuwa uku.

Da wannan ne Canisius ke fatan wasu daga cikin 'ya'yansa su gaji wannan sana'ar dan dogaro da kansu a nan gaba, ko da yake sarrafa madarar cukwi a tsaunukan gabashin cKwangon sai an zage dantse kamar yadda Canisius ke dakon kilo 30 na cukwin sannan ya yi tafiya mai nisan kilo mita biyar kafin ya kai ga shi.

Sauti da bidiyo akan labarin