1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Interpol ta aika sammacin ka Carlos Ghosn

Abdoulaye Mamane Amadou
January 2, 2020

Hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa Interpol ta aika wa hukumomin kasar Lebanon takardar sammacin kama tsohon shugaban kamfanin kera motocin Nisan da ya tsere daga Japan.

https://p.dw.com/p/3VbaU
Libanon Carlos Ghosn in Beirut
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Moukarzel

Hukumomi a Lebanon sun tabbatar da samun sammacin kama Carlos Ghosn, tsohon shugaban kamfanin kera motocin nan na hadin gwiwa Nisan daga hukumar yan sanda ta kasa da kasa wato Interpol.

Tuni jami'an tsaron kasar suka sanar da samun sammacin kama Ghosn, sai dai har yanzu ba a mikawa hukumar shari'ar kasar ba, a cewar majiya mai tushe.

Shi dai Carlos Ghosn ya gudu ne daga kasar Japan inda yake jiran hukuncin kotu a daidai lokacin da hukumomi suke tsare da shi bisa zargin aikata laifuka da dama ciki har da almundahana, kana daga bisani ya sauka a kasar Lebanon a farkon wannan makon.