Sambo Dasuki zai gurfana gaban kotu | Labarai | DW | 25.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sambo Dasuki zai gurfana gaban kotu

Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya ta yi karar tsohon mai baiwa shugaban kasar shawara kan tsaro Kanar Sambo Dasuki kan mallakar makaman da ba su da rijista.

Mai magana da yawun hukumar tsaron ta farin kaya wato DSS Tony Opuiyo ya ce sun gano makaman ne bayan da ta samu wasu bayanai na sirri kan wannan batu, wanda hakan ya kai ga bincike gidajensa da ke Abuja da Sokoto a watan jiya har ma aka yi masa daurin talala.

Baya ga batun makamai, DSS din ta ce ta sami wasu sabbin motoci a gidan Kanar Dasukin ciki kuwa har da masu sulke wanda ya gaza yin cikakken bayani game da yadda aka yi ya mallake su.

Hukumar har wa yau ta ce ta gano cewar Kanar Dasukin ya aikata wasu abubuwa da ka iya zama barazan ga sha'anin tsaro a Najeriya wadda dama ke fuskantar kalubale na tsaro musamman a arewacin kasar.