Samatha Power za ta kai ziyara a Najeriya | Labarai | DW | 21.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Samatha Power za ta kai ziyara a Najeriya

Jakadiyar Amirka a Majalisar Ɗinkin Duniya samtha Power za ta gana da shugaba Muhammad Buhari domin tattauna rikicin Boko Haram.

An shirya a yau jakadiyar za ta isa a birnin Abuja na Tarayar Najeriya inda za ta gana da shugaba Muhammad Buhari.Kafin daga bisani ta gana da shugabannin siyasa da na farar hula da kuma sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu domin tattauna rikcin Boko Haram.

Kana kuma ana sa ran samantha za ta kai ziyara a yanki arewa maso gabashin na Najeriya domin ganewa idonta halin da 'yan gudun hijirar wanda tashin hankalin na Boko Haram ya tilasta wa barin matsugunansu.Tun Farko Jakadiyar ta kai ziyara a ƙasar Kamaru inda ta gana da shugabannin ƙasar wanda a can ne ta sanar da cewar Amirka za ta ba da taimakon kuɗaɗe ga ƙasashen yankin tafki Chadi domin yaƙi da Boko Haram.