Samarwa marasa galihu ilimi a Ghana | Zamantakewa | DW | 09.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Samarwa marasa galihu ilimi a Ghana

'Yan mata 'yan shekaru 6 zuwa 18 da ke cikin anguwannin mara sa galihu sun fara amfana da wani shirin koyar da kimiyya da aka kirkiro da zummar ilmantar da su.

Shirin dai wata matashiya 'yar shekaru sama da 30 ce ta kaddamar, inda fiye da 'yan mata 50 da shekarun su ke tsakanin 6 zuwa 18 ne ke tattare acikin wani aji a anguwar Nima, daya daga cikin anguwannin masu matsakaicin karfi a birnin Accra, inda suke daukan darasin na komputa. Kamar yadda wannan daliba rRegina Agyare, wace ta kammala jami'a, a lokacin da take koyar da dalibanta. Bayan koyarwar, ta na kuma tafiyar da shirin da ake kira "Tech Needs Girls Ghana Initiative", wanda ta kirkiro bayan ta yi murabus daga aikin ta na banki a shekarar 2012, tare da zummar azurta yawancin matasa da ilimin komputa. Inda ta yi karin haske.


"Muna farawa ne da koyar da su muhimmun ilimin farko na komputar, domin su fahimci abubuwan da za su kirkiro a nan gaba, don amfanar da zamantakewa, ko kuwa samar wa kansu wani guzuri ta fuskar tattalin arziki"
Regina ta kara da cewa kawo yanzu dai shirin ya samu gagarumin ci gaba, ba a birnin Accra kadai ba, amma kuma har a wasu sassa daban da aka fara shi. Wasu daga cikin daliban sun nuna taimakon da suka samu daga wannan shiri a bangaren duniyar komputa.


"Ana koyar damu ne tare da amfani da wata fasaha ta musamman, kuma da farko yawancin mu matan na tsoron zama ajin komputa, tare da takwarorin mu maza. Amma a yanzu da taimakon shirin "Tech needs girls", muna fafatawa da su, har mu kan fi su kokari. K uma a yanzu ma na fahimci dalilin daya sa nake amfani da wayar salula. Tech needs girls ya koyar damu yadda ake amfani da shafukan yanar gizo da kuma kirkiro su, wanda ya kasance wani bangare ne da maza suka fi kwarewa, amma a yanzu mun fara dama wa da su"


Duk da cewa Regina bata samu lamarin da sauki ba kamar wannan 'yan mata, ta dai kafa kamafanin na kirkiro shafukan yanar gizon ne, tare da taimakon 'yan uwa wadan da suka tanadar mata da komputar tafi da gidanta da euro 500. A halin yanzu ta na da ma'aikata 30. Inda Isaac Quaye ke cewa.

"Wannan ba karamin ci-gaba bane, kasancewar tun da na zo babu abinda abinda na ke gani face samun ci gaba a bangaren 'yan matan, da kuma zurfin ilimin su fiye da kima"


Burin Regina dai shine kawo sauyi a rayuwar yawancin 'yan mata a Afrika, ta fuskar ilimin komputa, kuma duk da cewa ta na fuskantar kalu balen kudi, ta ce, fadada wannan shirin gaba da iyakokin kasar Ghana shine muradinta.