1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin inganta tsaro a yankin Sahel da Sahara

Uwais Abubakar Idris RGB
June 19, 2018

Kwararu a kan harkar tsaro daga kasashen yankin Sahel da Sahara sun gudanar da wani taro a kokarin shawo kan matsalolin ayyukan ta’ddanci na Boko Haram da IS a kasashe 28 na yankin.

https://p.dw.com/p/2zsMZ
Mali Soldaten ARCHIV
Hoto: dapd

Taron ya mayar da hankali kan matsaloli kama daga ayyukan ta'addanci da ake zargin kungiyar Boko Haram da kuma yadda mayakan kungiyar nan ta IS ke samun shiga a kasashen yankin Sahara da Sahel, akwai kuma batun fadan makiyaya da manoma da ke tada hankali ainun a tsakanin kasashen. Batun kasar Libiya da a ke wa kalon wata kafa ta samun haramtattun makamai ya dauki hankulan mahalarta taron na birnin Abuja a Najeriya. Wannan ya sanya ma'aikatar tsaron Najeriya yi wa ‘yan jaridu bayani a kan muhimmancin taron da ma abubuwan da ministocin za su tattauna a taron na yini biyu.

Afrika Mali Hirte Herde Rinder Symbolbild Konflikt Mali Burkina Faso
An nemi magance rikicin manoma da makiyayaHoto: Fotolia

Kodayake kasashen sun hallara don wannan taro amma ana nuna damuwa kan rashin hadin kai a matsayin babban dalilin da ya sanya fuskantar jan kafa a kan matsalar, musamman a tsakanin kasashen Sahara da Sahel. A can baya dai kasashen sun gudanar da irin wadannan tarurruka da nufi ko fata ta samun kai wa da gano bakin zaren.

Amma batun da ya kunno kai na kungiyar IS a yankin Sahel da Sahara na zama babbar barazana, lamarin ya sanya daukan mataki. Ana fatan wannan taron karo na bakwai da ya hada kasashe irin su Somaliya da Libya zai taimaka wajen shawo kan wannan matsalar.