1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samar da na'urar nadar bayanai ga 'yan sandan Amirka

December 2, 2014

Wannan mataki na zuwa ne bayan da wani dan sandan Amirka Darren Wilson farar fata ya harbe Micheal Brown bakar fata da baya dauke da bindiga.

https://p.dw.com/p/1DxxM
Symbolbild Polizeigewalt in den USA
Hoto: Getty Images/AFP/J. Samad

Shugaba Barack Obama na Amirka ya bayyana a jiya Litinin cewa za a kashe dalar Amirka miliyan 75 cikin abinda gwamnatin tarayya ke kashewa inda za a samar da wata na'urar nadar bayanai da 'yan sanda dubu hamshin za su rika makalawa a jikinsu, ta yadda za a rika samun bayanai kan yadda mu'amalarsu take da fararen hula.

Shugaban ya bayyana haka ne a wani zama da yayi da majalisar ministocinsa da kungiyoyin fararen hula da ma wasu jami'ai na bangaren shari'a. Wannan yunkuri kuwa na zuwa ne bayan da masu shari'a suka gaza kama dan sandan na Amirka farar fata da ya harbe matashi Micheal Brown bakar fata dan shekaru 18 wanda baya dauke da makami .

Dubban Amirkawa ne dai suka fito dan nuna adawarsu da hukuncin alkalan inda suka gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar, inda tafi muni a Furguson da ke jihar Missaouri.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu