Samar da mafita ga rikicin Siriya | Labarai | DW | 25.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Samar da mafita ga rikicin Siriya

Bayan dage taron Geneva na kasa da kasa kan rikicin Siriya a karo daban-daban, a karshe an amince da ranar 22 ga watan Janairu domin gudanar da taron.

Wakilan gwamnatin kasar Siriya da na 'yan tawaye za su gana a birnin Geneva na kasar Switzerland a ranar 22 ga watan Janairu mai zuwa domin lalubo bakin zaren kawo karshen yakin basasar da ya barke a kasar sama da shekaru biyu.

A wata sanarwa da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya fitar, ya nunar da cewa a karshe an amince da wannan rana ta 22 ga watan Janairun 2014 domin ganawar bangarorin biyu, bayan da akai ta sanya ranar ganawar ana kuma dage wa.

Ban, ya kuma yabawa Jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar kasashen Larabawa kan magance rikicin Siriya, Lakhdar Brahimi, da kuma kasashen Amirka da Rasha bisa kokarin da suka yi wajen shirya taron sasanta rikicin na Siriya.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Saleh Umar Saleh.