Sama da mutane 200 sun halaka a bala′in tsunami | Labarai | DW | 23.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sama da mutane 200 sun halaka a bala'in tsunami

Lamarin da ya faru a Indonesiya ya shafi yanki a tsakanin Java da Sumatra, akwai dai wasu mutanen da suka bace da ba a kai ga sanin inda suke ba yayin da gidaje daruruwa da otel-otel suka rushe.

Sama da mutane 200 ne suka rasu wasu daruruwa suka samu raunika sakamakon aukuwar guguwa da ruwan sama mai karfi hadi da girgizar kasa da suka tada Tsunami wanda ya shafi bakin ruwa a yankin mashigar teku na Sunda a yammacin ranar Asabar. Lamarin ya shafi yanki a tsakanin Java da Sumatra, akwai dai wasu mutanen da suka bace da ba a kai ga sanin inda suke ba yayin da gidaje daruruwa da otel-otel suka rushe kamar yadda hukumar da ke sa ido kan afkuwar bala'oi (BNPB) ta bayyana.

A cewar masanan kimiya dai an samu fashewar wani tsauni mintuna 24 daga bisani aka samu kuma bala'in na Tsunami. Mutanen da abun ya shafa dai sun hadar da na yankin Padenglang da kudancin Lampung da Serang, wadanda ke a kasa da kilomita 150 daga yammacin Jakarta.