Saliyo: Dan takarar adawa na kan gaba | Labarai | DW | 11.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saliyo: Dan takarar adawa na kan gaba

Kwarya-kwaryar sakamakon zaben shugaban kasa a Saliyo na nuni da cewar Julius Maada Bio, shi ne ke kan gaba a sahun wadanda suka kai dakyar, bisa ga sakamako yanzu.

 

Bio mai shekaru 53 da haihuwa, kuma mutumin da ke wakiltar babbar jam'iyyar adawa ta SLPP, shi ne ke kan gaba da yawan kuri'u sama da kashi 43 daga cikin kashi 75 na yawan kuri'u da aka kidaya kawo wannan rana ta Lahadi, kamar yadda shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Mohamed Nfa Allie Conteh, ya nunar.

Sai dai babban abokin kalubalantar Bio, Samura Kamara mai shekaru 76 da haihuwa da ke wakiltar jam'iyyar APC mai mulki, na dab dashi da kashi 42.

Bisa dukkan alamu dai, ba za'a kaucewa tafiya zagaye na biyu na zaben shugaban kasar ba, tunda babu dan takara da ya samu kashi 55 da ake bukata na lashe zaben kai tsaye ba.

Zaben kasar baki daya da ya gudana a kasar ta yankin yammacin Afirka ranar 7 ga wata dai, na zuwa ne bayan farfadowar da kasar ta yi daga cutar Ebola da ta haddasa mutuwar mutane wajen dubu hudu tsakanin 2014-2016, da mummunar zabtarewar kasa da ta binne daruruwan mutane a shekarar data gabata.