Saliyo: An fara zaman makoki na mako daya | Labarai | DW | 16.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saliyo: An fara zaman makoki na mako daya

Gwamnatin kasar Saliyo ta sanar da zaman makoki na mako daya domin jimamin mutanen da suka rasu a ambaliyar ruwa.

Al'ummar kasar Saliyo sun fara zaman makoki na kwanaki bakwai a yau laraba domin jimami da nuna alhini ga mutanen da suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa da suka yi sanadiyar mutuwar daruruwan jama'a.

Da yammacin yau za'a gudanar da taron addu'oi na mabiya addinai daban daban a babban filin wasa dake Freetown babban birnin kasar inda iftila'in ya auku.

Ya zuwa yanzu an an gano gawarwakin mutane 297 da suka hada da kananan yara 109.

Ba dai kai ga tantance adadin mutanen da suka rasu ba. Da farko dai ministan lafiya na kasar yace adadin ya kai mutum 500 yayin da dama kuma har yanzu ba'a gano su ba.

A gobe Alhamis za'a yi jana'izar mamatan.