1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tilastawa yara shiga aikin soja

February 13, 2019

Rayuwar Ishmael Alfred Charles, da aka tilastawa shiga aikin soja a kasar Saliyo a yayin da ya ke dan shekara 14 da haihuwa, idanunsa sun ga munin yakin basasar kasar a karkashin 'yan tawaye

https://p.dw.com/p/3DIbC
Somalia Kindersoldaten
Hoto: Getty Images/AFP/M. Dahir

Bayan yakin ne ya je jami'a inda ya koyi ilimin lakantan zaman lafiya da iya warware takaddama. Yanzu ya kafa gidauniyar da ke samarwa yara masu fama da cuta ta musanman magani.

Yakin basasa na sama da shekaru 11 a kasar Saliyo, ya shafi rayuwar dubban yara masu kananan shekaru da aka tilastawa shiga aikin soja, Ishmael Charles na daya daga cikinsu da ya zabi juya munin abin da ya gani zuwa kyawawan ayyuka, shin ko mai ya sanya masa wannan tunani?

''Abin da ya zaburar da ni shi ne, yadda na ga wahalhalu da rayuwar jama'a ta shiga a lokacin rikicin yakin, akwai matsala ta rashin maganin asibiti ko kulawa a wancan lokacin, daga nan ne na kudiri niyyan taimakawa jama'a, ba zan sake zama silar haddasa wa dan adam kowanne na'ui na wahala ba, abin da zance ya zaburar dani kenan''

Saliyo na fama da karancin asibitoci a sanadiyar yakin basasa da kuma bullar annobar Ebola bayan rikicin. Duk wanda ya yi katarin gamuwa da cutar da ta fi karfin asibitocin kasa, sai dai ya nemi magani a kasashen Ghana ko Indiya, wanda ke da matukar tsada.

Amma Charles ya sha shawo kan lamarin inda ya ke shiga don samun tallafin da za a iya samarwa yara magani a duk kasar da ta kama. Ya fi anfani da shafukan internet don jan hankulan masu son bayar da taimakon. A nan ya yi karin bayani kan irin manyan kalubalen da ya ke cin karo dasu.