Salif Diallo ne shugaban majalisar Burkina | Labarai | DW | 31.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Salif Diallo ne shugaban majalisar Burkina

An zabi Salif Diallo tsohon na hannun daman hambararren shugaban kasar Burkina Faso Blase Compaore a matsayin shugaban majalisar dokokin kasar.

Salif Diallo mai shekaru 58 a duniya wanda 'yan majalisar dokokin kasar suka zaba kwanaki kalilan bayan rantsar da Roch Marc Cristian Kabore a matsayin sabon shugaban Burkina Faso.

Dukkanin mutanen biyu dai nada daga cikin mutanen da ke a kan gaba wajen kafa jam'iyyar MPP wacce ta lashe zaben kasar da gagarumin nasara a watan daya gabata. Sannan a hannu daya sun kasance na hannun daman Blaise Compoare da aka hambarar da gwamnatinsa a watan Oktoban shekara 2014 sakamakon aniyar yin tazarce.

Nasarar da Daillo ya samu a majalisar Burkina Faso na nuni da cewar mai yuwane mutanen biyu su janyo masu goyon bayan tsohon shugaban kasar Blaise Compaore kusa dasu a harkokin mulkin kasar.