1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kawata shimfidun gadajen amare

January 16, 2019

Matashiya Asma’u data kammala digirinta ta rungumi sana’ar kawata shinfidun gadajen amare inda ta ce sana’ar ta gama mata komai na rayuwa sakamakon yadda sana’ar ke tashe.

https://p.dw.com/p/3BfjW
Stock-Foto Bettwäsche
Hoto: Colourbox/Mykola Komarovskyy

Matashiyar ta ce ta tsunduma cikin harkokin sana'ar ne tun tana ‘yar karama inda bayan kammala jami'a ne tayi tunani dangane da irin yanayin zamani da kuma irin sana'ar da ta dace da wannan zamanin.

Duk da yake bata yi wata wata ba ta soma wannan sana'a  ta samar da kayan kawa ga amare musamman a birnin Sakkwato kafin ta fara samun kwastomomi daga sassa daban-daban sakamakon tattalata hajarta a shafukan  sada zumunta na yanar gizo.

Yanzu haka dai wannan sana'a ta karbi Asma'u hannu bibbiyu lamarin da ya kaita ga bude kanfanin ta mai suna Asmee Bridal Zone a birnin na Sakkwato.

Matashiyar ta ce ‘yan mata da dama ne ta ke baiwa horo dangane da sha'awar da suke nunawa ga wannan sana'a tata.