1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yamutsi a Isra'ila saboda canza doka

Abdourahamane Hassane
March 12, 2023

A Isra'ila, dubun dubatar jama'a sun yin zanga-zanga a mako na goma a jere domin nuna adawa da sake fasalin tsarin shari'a da gwamnati ke kokarin aiwatarwa.

https://p.dw.com/p/4OYua
Israel I Drei Verletzte durch Schüsse im Zentrum von Tel Aviv
Hoto: Oded Balilty/AP/picture alliance

Kafofin yada labarai na Isra'ila sun rawaito cewar sama da mutane dubu dari sun halarci gangamin a tsakiyyar birnn Tel Aviv saboda gwamnatin Benjamin Netanyahu na shirin gaggauta aiwatar da ayyukan majalisar dokoki a yau Lahadi, ranar farko ta mako a Isra'ila, don ingiza wannan shiri na sauye-sauye tsarin sharia a kasar. Wannan garambawul na alamuran sharia a israila zai baiwa gwamnatin ikon nada alkalai a maimakon kotun kolli, da kuma wasu sauye-sauyen abin da jamaa ke cewa taka tsarin dimukaradiyya ne