Sakataren harkokin wajen Amurka na yin ziyara a Gabas ta Taskiya
April 7, 2013Sakataran harkokin wajen Amurka John Kerry ya soma wata ziyarar aiki a wannan Lahadi a ƙasar Turkiya. A wani mataki na rangadi na kwanaki goma da zai yi a cikin ƙasashen Gabas ta Tsakiya da Ingila da Japan da kuma yankin Asiya.
Muhimman bututuwan da babban jami'in diflomasiyyar na Amurka zai mayar da hankali a kansu a lokacin ziyara, shi ne zancen tashin hankalin da ake yi a Siriya da rikicin Koriya ta Arewa da kuma na yankin Gabas ta Tsakiya tsakanin Israi'la da Falasɗinu. Masu lura da al'amuran yau da gobe na furta kalamun cewar Amurka ta zaɓu wajen ganin an shawo kan rikicin na yankin Gabas ta Tsakiya, ta hanyar sake farfaɗo da shirin tattaunawa na gaba da gaba tsakanin Falasɗinu da Isra'ila.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal